'Boko Haram ba ta kashe 'yan matan Chibok ba'

Shugaba Jonathan ya gana da iyaye da wasu 'yan matan Chibok da suka tsira a watan Yuli, bayan an sace su a watan Afrilu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Jonathan ya gana da iyaye da wasu 'yan matan Chibok da suka tsira a watan Yuli, bayan an sace su a watan Afrilu

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce ya yi imanin cewa mayakan Boko Haram ba su kashe 'yan matan nan fiye da 200 da suka sace daga makaranta a garin Chibok ba.

Mr. Jonathan ya fadi hakan ne a cikin wata hira da ya yi da wani gidan tallabijin mai zaman kansa da ke kasar wato AIT wadda aka watsa a ranar Alhamis.

Shugaban ya kuma ba da tabbacin cewa za a kwato sassan jihohin Yobe da Adamawa da ke karkashin Boko Haram nan da mako mai zuwa.

''Mun yi alkawalin za mu gano 'yan matan nan kuma abin farin cikin shi ne ba su kashe su ba domin 'yan ta'adda kan nuna wadanda suke kashewa domin tsoratar fararen hulla da sauran al'umma.

Don haka wadannan 'yan matan suna nan raye kuma yanzu muna rage fadin yakin da Boko Haram ke iko da su muna kara kusantarsu don haka tabbas za a gano su." In ji Jonathan.

Inda ya kara da cewa "Babu shakka za su yi garkuwa da 'yan matan, hakan ne ya sa ake yakin bisa ka'idojin kasa-da-kasa domin ba zai yiwu a kutsa kawai da manyan bindigogi mu share komai ba. Wannan ne yasa yakin ke tafiyar hawainiya.''

Shugaban kasar ya amince cewa da fari gwamnatinsa ba ta dauki batun kungiyar ta Boko Haram da muhimmanci ba.

Sai dai wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok sun ce sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba, sai sun ga 'ya'yan nasu da rai.

Yayin da ita kuma kungiyar da ke fafutukar ganin an kubutar da 'yan matan ta ce za ta yi nazi kan kalaman shugaban kasar.