An yi wa Kano Pillars fashi da makami

Ba a san ko lamarin zai shafi wasansu na Premier da na kofin Zakarun Afrika ba

Asalin hoton, Kano Pillars Web Site

Bayanan hoto,

Ba a san ko lamarin zai shafi wasansu na Premier da na kofin Zakarun Afrika ba

An yi wa 'yan Kano Pillars fashi da makami a Abaji da ke Abuja a kan hanyarsu ta zuwa Owerri inda kuma aka raunata wasu 'yan wasan daga cikinsu.

'Yan fashin sun kwace wa 'yan wasan kayayyaki suka kuma raunata 'yan wasa biyar daga cikinsu da harbin bindiga.

'Yan wasan da aka harba, sun hada da Gambo Mohammed da Ogbonaya da Eneji Otekpa da Murtala Adamu da kuma Moses Ekpai.

Rahotanni sun ce 'yan wasan suna samun sauki kuma ana ganin ba dadewa ba za a sallame su.

'Yan fashin sun karbe wayoyin salula da sauran kayayyaki na 'yan wasan.

Zakarun Premier din sun gabatar da bukatarsu ga kwamitin gasar Premier ta Najeriya ta neman dage wasansu da ke tafe da Heartland saboda harin da aka kai musu.

Ya zuwa yanzu dai ba a san ko lamarin zai shafi wasan nasu na Premier da kuma na kofin Zakarun Afrika ba.