'Gawawwakin mutane 68 na yashe a Djaba'

Mutane na gujewa rikicin Boko Haram

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutane sama da miliyan daya ne suka tserewa rikicin Boko Haram, a arewa maso gabashin Nigeria.

A Najeriya, wani mazaunin Damboa a jihar Bonon a Nigeria ya shaida wa BBC cewa an kasa binne gawawwakin mutane 68 da aka hallaka a kauyen Djaba.

Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kashe mutanen a wani harinda suka kai kauyen a ranar Talatan da ta gabata.

Wasu mazauna garin Damboa da bashi da nisa da kauyen sun je domin binne gawawwakin, amma da suka ji labarin 'yan Boko Haram din na tafe yasa suka gudu suka bar gawawwakin a yashe, a cewar mutumin.

Bayanai dai sun nuna cewa wadanda aka kashe yawancinsu maza ne tsofafi da kananan yara.

'Yan bindigar sun kuma kona daukacin gidajen kauyen a yayin harin kai harin.

Sai a yanzu ake samun labarin saboda babu hanyar samun labarai a kauyen har sai da mutanen da suka tsira suka isa Maiduguri.

Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane fiye da 13,000 cikin shekaru shida.

Rikicin Boko Haram wanda aka soma a Nigeria a yanzu ya shiga makwabtan kasashe kamar su Chadi da Kamaru da kuma Nijar.