An fara yi wa mata bita kan Zabe

'Yan takarar shugaban kasa a Nigeria

Asalin hoton,

Bayanan hoto, Wasu dai na ganin cewa, hukumar zaben Nigeria ba ta wayar da kan al'uma yadda za su kada kuri'a.

Yayin da babban zaben Nigeria ke kara karatowa, wasu yan siyasa sun dukufa wajen fadakar da jama'a yadda za su kada kuri'un su cikin sauki ba kuma tare da sun bata su ba.

Wasu mutanen na ganin hukumar zaben kasar INEC ta gaza wajen wayar da kan mutanen, shi ya sa ma yan siyasa ke yi, to sai dai INEC din tace abun ya mata yawa ita kadai, amma fa tana iya kokarin ta.

An dai gudanar da a jihar Jigawa, dan fadakar da mata abubuwan da ya kamata su yi ranar zabe.

Cikin abubuwan da aka wayar musu da kai akwai illar da ke tattare yin lalle ko kunshi a 'yan yatsu da mata suke yi, inda masu bitar suka ce hakan na janyo matsala ya yin dan gwala kuri'a.

Sai kuma gargadin su da aka sake yi, kan batun saida kuri'arsu, wadda take a matsayin 'yancinsu.