NFF ta kori Stephen Keshi daga aiki

Keshi ne ya jagoranci Super Eagles ta lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015
Bayanan hoto, Keshi ne ya jagoranci Super Eagles ta lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015

Hukumar kwallon kafar Nigeria NFF ta sallami Stephen Keshi daga aikin horas da tawagar kwallon kafar Nigeria nan take.

Tuni kuma aka maye gurbinsa da Salisu Yusuf -- wanda yake mataimakin koci kafin a sallami Keshi daga aikin.

Hakan ya biyo bayan kwamitin bincike da hukumar ta nada kan zargin zawarcin aikin kocin tawagar kwallon kafar Ivory Coast da Keshi ya nema a makwonni biyu da suka wuce.

Keshi ya ce an mika takardunsa cikin masu son aikin horas da Ivory Coast ba tare da ya sani ba.

Hukumar kwallon kafar Ivory Coast ce ta wallafa sunayen masu horar da kwallon kafa sama da 50 da suke zawarcin kocin tawagar kwallon kafar kasar, ciki har da sunan Keshi.

Shaibu Amodu wanda aka nada daraktan tsare-tsare na hukumar a makwon jiya, zai dunga sa ido kan yadda za a gudanar da Super Eagles.

A cikin watan Afirilu ne Keshi ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da NFF domin ya kara jagorantar Super Eagles.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta ce za ta nada sabon koci da zai jagoranci tawagar kwallon kafar kasar nan bada dade wa ba.