Wikki ta ziyarci Dolphins a gasar Premier

Wasannin mako na 16 da za a buga a gasar cin kofin Premier Nigeria

Asalin hoton, glonpfl Twitter

Bayanan hoto, Wasannin mako na 16 da za a buga a gasar cin kofin Premier Nigeria

Dolphins ta karbi bakuncin Wikki Tourists a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 16 da za su kara ranar Lahadi a Fatakwal.

Sauran wasannin da za a buga sun hada da karawa tsakanin Kano Pillars da El-Kanemi Warriors, Sharks ta karbi bakuncin Nasarawa United, Akwa United da Rangers.

Wasan da zai ja hankalin masu sha'awar kwallon kafa shi ne tsakanin Enyimba da Aba Warriors.

Ga wasannin mako na 16 da za a fafata:

  • Dolphins vs Wikki Tourists ??
  • Giwa FC vs Heartland ??
  • FC Ifeanyiubah vs Shooting Stars ??
  • Sharks vs Nasarawa United ?
  • Enyimba vs Abia Warriors ?
  • Bayelsa United vs Warri Wolves
  • Lobi Stars vs Sunshine Stars?
  • Akwa United vs Rangers ?
  • Kano Pillars vs El-Kanemi Warrior