An hallaka mutane 44 a hare-haren Jos

Bam ya tashi a shagon Shagalinku lokacin mutane da bude baki
Bayanan hoto, Bam ya tashi a shagon Shagalinku lokacin mutane da bude baki

Akalla mutane 44 ne suka rasa rayukansu sannan wasu 47 suka jikkata bayan tashin tagwayen bama-bami a Jos, babban birnin jihar Plateau da ke tsakiyar arewacin Najeriya a daren Lahadi.

Daya daga cikin bama baman ya tashi ne a masallacin 'yan taya a lokacin da shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'a Wa Ikamatu Sunnah ta kasa, Sheik Sani Yahaya Jingir, yake gudanar da tafsirin Al'Qur'ani, al'amarin da aka ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 sannan wasu da dama sun jikkata.

An dai ce wani mutum ne ya zo masallacin a inda ya zaro bindiga ya bude wuta a kan mutane kafin ya fara jefa gurneti cikin masallacin, sannan bam din ya tarwatse da shi.

Kafin tashin bam din a masallacin, sai da wani ya fara tashi a gidan cin abinci da ke kan titin Bauchi a birnin, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23.

Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce mutane 47 ne suka jikkata a hare-haren guda biyu.