Boko Haram ta kashe mutane 1,000 a bana

Tun fara rikicin Boko Haram mutane fiye da 13,000 ne suka mutu a Nigeria.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Tun fara rikicin Boko Haram mutane fiye da 13,000 ne suka mutu a Nigeria.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce daga watan Janairu zuwa yanzu kungiyar Boko Haram a Nigeria ta kashe fareren hula fiye da 1,000 a jihohin arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bukaci gwamnatin Nigeria da ta ba da fifiko kan kare fararen hula a yakin da sojojinta suke yi da 'yan Boko Haram.

Kungiyar ta ce hare-haren 'yan Boko Haram sun karu tun daga watan Janairu abin da ya janyo karuwar mutuwar fararen hula.

Sanarwar ta Human Rights Watch ta kara da cewa ta cimma wannan alkaluman ne bayan samun bayanai daga wadanda suka shaida lamarin da kuma sharhi daga kafafen yada labarai.

Inda ta kara da cewa tun daga karshen watan Janairun da ya gabata mutanen da suka tsere daga jihohin Yobe da Adamawa da kuma Borno a arewa maso gabashin kasar sun bayar da labarai masu tayar da hankali game da rashin imanin da 'yayan kungiyar ta Boko Haram suka aikata.

Sanarwar ta zargi sojoji da aikata laifukan keta hakkin bil'adama a wani kauye, zargin da ta ce hukumomin sojin kasar sun ce sun fara bincike a kansa.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a Nigeria.