Enyimba da Abia Warriors sun tashi 2-2

Sakamakon wasan mako na 16 a gasar Premier Nigeria

Asalin hoton, HeartlandFC twitter

Bayanan hoto, Sakamakon wasan mako na 16 a gasar Premier Nigeria

Enyimba International da Abia Warriors sun tashi wasa 2-2 a gasar Premier wasan mako na 16 da suka kara ranar Lahadi a Aba.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Kano Pillars ta doke El-Kanemi Warriors da ci daya mai ban haushi a Kano, a inda Giwa FC ta samu nasara a kan Heartland da ci 2-1.

Fafatawa tsakanin Dolphins da Wikki Tourist tashi wasa suka yi kunnen doki a Fatakwal, yayin da karawa tsakanin Lobi Stars da Sunshine shi ma suka buga 1-1.

Ga sakamon wasannin da aka buga a gasar Premier Nigeria:

  • Enyimba 2-2 Abia Warriors
  • Bayelsa United 2-0 Warri Wolves
  • Giwa FC 2-1 Heartland
  • Kano Pillars 1-0 El-Kanemi Warriors
  • Akwa United 2-0 Rangers
  • FC Ifeanyiubah 1-0 Shooting Stars
  • Dolphins 1-1 Wikki Tourists
  • Sharks 0-0 Nasarawa United
  • Lobi Stars 1-1 Sunshine Stars
  • FC Taraba 0-0 Kwara United