Rashin yin tiyata na kashe fiye da rabin mutanen duniya

Masu bincken sun ce akwai bukatar horas da ma'aikatan tiyata.
Bayanan hoto, Masu bincken sun ce akwai bukatar horas da ma'aikatan tiyata.

Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi biyu cikin uku na mutanen duniya ba sa iya samun tiyata cikin sauki da inganci.

Masu binciken-- wadanda suka kwashe shekara guda suna yin nazari a kasashe dari -- sun gano cewa talakawa da masu matsakaicin hali na mutuwa sakamakon cututtukan da za a iya yin maganinsu cikin sauki irin su karaya da matsalolin da ake fuskanta a lokacin haihuwa.

Masu binciken -- wadanda suka wallafa shi a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet -- sun yi kira da a zage dantse wajen samar da kayayyakin yin tiyata, fannin da, a cewarsu, aka yi watsi da shi.

Sun kara da cewa za a shawo kan matsalar ce idan aka ba da horo ga likitocin da ke yin tiyata da samar da alluran da ke kashe zafi da makamantansu.