Damasak:Jami'an Nigeria sun yi baki-biyu

Sojin Nigeria na cigaba da kokarin kwato sauran garuruwan da ke karkashin ikon Boko Haram

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojin Nigeria na cigaba da kokarin kwato sauran garuruwan da ke karkashin ikon Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta yi baki-biyu a kan zargin da aka yi cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun sace yara kusan 500 daga garin Damasak na jihar Borno.

Shugaban cibiyar da ke bayar da bayanai kan ta'addanci, Mr Mike Omeri ya shaida wa BBC cewa duk da yake lamarin ya faru, amma ba yanzu ya faru ba, yana mai cewa yawan mutanen da aka sace ba su kai 500 ba.

Sai dai rundunar sojin kasar ta musanta rahotannin da ke cewa an sace yaran kwata-kwata, tana mai cewa hakan bai faru ba.

Mukaddashin kakakin rundunar sojan kasa ta Nigeria Kanar Sani Usman Kuka-sheka, ya shaidawa BBC cewa "babu birbishin gaskiya ko kadan cikin wannan labari na bacewar yara har kimanin 500."

A ranar Talata ne wani dan garin na Damasak ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa ba su ji duriyar wadannan yara ba, da ya ce yawansu ya kai 500, kuma ciki har da kaninsa, suna zargin cewa mai yiwuwa 'yan Boko Haram sun yi awon gaba da su.

A baya dai kungiyar Boko Haram ta sha sace mutane a duk lokacin da ta kai hare-hare domin saka su cikin mayakanta.