An tono gawar Thomas Sankara a Burkina Faso

Mutane na rububin zuwa wajen da ake tono gawar Thomas Sankara
Bayanan hoto, Mutane na rububin zuwa wajen da ake tono gawar Thomas Sankara

A kasar Burkina Faso, an fara aikin tono gawar tsohon shugaban kasar, Thomas Sankara, wanda ya mutu shekaru 28 da suka gabata.

Wasu likitocin kasar da na Faransa za su gudanar da gwajin kwayar halitta domin tabbatar da cewa gawar tasa ce, haka kuma za a binciki abin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Mahukuntan kasar dai sun dauki wannan matakin ne sakamakon matsin-lambar da iyalan Thomas Sakaran ke yi game da bukatar hakan.

Kazalika za a tona gawawwakin wasu mutune 12 da aka hallaka tare da Mr. Sankara domin yi musu irin wannan gwajin.

Thomas Sankara dai soja ne mai ra'ayin Markisanci da ya jagoranci fafutukar 'yanta kasar Burkina Faso, kuma Blaise Compore ne ya hambare gwamnatinsa a shekarar 1987, wanda shi ma guguwar sauyi ta hambarar da shi a bara.