An bai wa 'yan Tunisia kyautar Nobel

Kungiyoyin da ke kare mulkin dimokradiyyar Tunisia sun lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kungiyoyin da ke kare mulkin dimokradiyyar Tunisia sun lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Kungiyoyin da ke kare mulkin dimokradiyya a Tunisia sun lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel saboda gudunmuwar da suka bayar wajen mika mulki.

An kafa kungiyoyin guda hudu ne a shekarar 2013 sakamakon kashe-kashen da ake yi da ke da dangataka da siyasa a lokacin da ake shirye-shiryen zaben kasar.

Kungiyoyin su ne: Tunisian General Labour Union da Tunisian Confederation of Industry, Trade and Handicrafts da Tunisian Human Rights League, da kuma Tunisian Order of Lawyers.

Shugabar kwamitin da ke bayar da kyautar, Kaci Kullmann Five, ta ce kungiyoyin sun bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci gaban dimokradiyyar kasar bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2011.

Kungiyoyin hudu sun fafata ne da kimanin mutane 273 -- cikin su har da shugabar kasar Jamus Angela Merkel da Paparoma Francis -- domin lashe kyautar.

Kaci Kullmann Five ta ce, "A lokacin da kasar Tunisia ta shiga halin tashin hankalin da ya nemi durkusar da ita sakamakon rikicin siyasa, an kafa wadannan kungiyoyi domin samar da zaman lafiya, da kuma 'yancin kare hakkokin jinsi da ra'ayin na addini".