Ban ya ce a agaji mutanen da boko-haram ta shafa

mutanen da mayakan  boko haram suka daidaita
Bayanan hoto, Mata da yara da dama ne rikicin boko haram ya raba da gidajensu a Najeriya

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya bukaci gwamnatin Najeriya ta taimaka wa mutanen da rikicin boko-haram ya ritsa da su.

Ya ce akawai bukatar a agaza ta fannin kiwon lafiya ta yadda za su samu natsuwa, musamman wadanda aka yi wa fyade.

Sojojin Najeriya da takwarorinsu daga kasashen da ke makabtaka da kasar sun kwace wasu garuruwa daga hannun mayakan boko-haram a watan Fabrairun da ya wuce.

Wasu mata da yaran da aka ceto daga mayakan kungiyar sun yi bayani a kan irin cin zarafin da aka yi musu, ciki har da fyade, yayin da wasu iyaye suka bayyana takaicinsu dangane da yanda ake tilasta wa 'ya'yansu su kai hare-haren kunar-bakin-wake.

Mr Ban Ki Moon ya ce ya yi matukar kaduwa da bayanan da ke fitowa daga bakin mutanen, kana ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta hanzarta wajen kula da su ta hanyar da magunguna da kwararrun da ake bukata.

A baya dai Majalisar Dinkin Duniyar ta soki mahakuntan Najeriya game da yadda take tunkurar rikicin boko-haram, tana cewa sojojin kasar na yin nawa wajen dakile ayyunkan kungiyar.