'Yan kasuwa sun zargi jami'an gwamnatin Sokkoto

Asalin hoton, sokoto govt

A jihar Sokkoton Najeriya wasu masu sayen motocin gwanjo da suka fito daga sassa daban-daban na kasar na zargin jami'an gwamnatin jihar mai-barin-gado da damfararsu kudi na miliyoyin Nairori.

Masu korafin dai sun ce tun a watan Febrairu wannan shekara ne gwamnatin ta yi musu gwanjon motoci, kuma suka biya kudadensu amma aka ki ba su motocin.

Daga bisani aka shaida musu cewa gwamnan jihar ya soke gwanjon, amma ba za a mayar musu da kudadensu ba, kamar yadda suka biya.

Jami'an gwamnatin da lamarin ya shafa dai sun ki cewa uffan kan lamarin lokacin da BBC ta tuntube su.