'Bello Chindo ba dan Boko Haram ba ne'

Jamian tsaron Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jamian tsaron Najeriya

Iyalan daya daga cikin mutanen da hukumomin tsaron Nijeriya suka kama a baya-bayan nan da ake zargi da kasancewa babban dan kungiyar Boko Haram sun musanta zargin da ake yi masa .

A kwanakin baya ne jami'an tsaro suka kama Bello Chindo a filin jirgin sama na Abuja, inda suka ce yana cikin 'yan Boko Haram su 100 da aka fi nema ruwa-a-jallo, wadanda aka wallafa hotunansu.

Sai dai 'yan-uwansa sun ce a iya saninsu babu ma hotonsa a cikin hotunan mutanen da ake nema.

Sun yi kira ga hukumomin Najeriya su sake shi, suna masu cewa bai kamata a ci gaba da tsare shi ba.