'Zai yi wuya a kawar da Boko Haram a Disamba'

Watan Disamba ne wa'adin kawo karshen hare-haren Boko Haram a Najeriya
Bayanan hoto, Watan Disamba ne wa'adin kawo karshen hare-haren Boko Haram a Najeriya

Cibiyar da ke samar da bayanai a kan rikice-rikice a Najeriya ta ce da wuya sojoji su kawo karshen hare-haren Boko Haram da kasar ke fama da su a watan Disamba.

Shugaban cibiyar, Air Commodore Yusuf Anas mai ritaya, ya shaida wa BBC cewa bisa yadda al'amura suke tafiya ba zai yiwu a kawo karshen ayyukan ta'addanci a watan Disamba kamar yadda shugabaMuhammadu Buhari ya sanya.

Ya ce har yanzu ma wasu kasashen yankin tafkin Chadi ba su kawo gudunmawarsu ba ta soji, abin da ya ce shi ma zai yi tarnaki wajen cimma burin a kayyadadden wa'adin.

Air Commodore Yusuf Anas ya kuma yi tsokaci kan masu ta-da-kayar baya na Biafra, yana mai bayyana su a matsayin wadanda ba su san abin da ya faru ba a lokacin yakin basasa, shi ya sa suke buga kujen yaki.