IMF zai soma ajiye kudi da Yuan na China
Asusun bada lamuni na duniya,IMF ya amince da sanya kudin China Yuan cikin kudaden kasashen waje da ake ajiyewa a asusunsa.
Wannan mataki dai tamkar na jeka na yika ne, amma kuma yana nuna irin karfin da China take kara samu a matsayin daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a tattalin arzikin duniya.
A yanzu Yuan, yabi sawun dalar Amurka da Euro da Yen na Japan da kuma Fan na Biritaniya cikin jerin kudaden da ake ajiyarsa a IMF.
Tun a shekarar da ta wuce ne China ta bukaci a saka Yuan a cikin jerin.
IMF ya ce sai a watan Okotobar 2016 ne matakin zai soma aiki.
Tattalin arzikin China shi ne na biyu mafi girma a duniya.