'Za mu rage hayakin da ake fitarwa'

Obama da Xi Jinping a lokacin taron

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, Obama da Xi Jinping a lokacin taron

Shugabannin manyan kasashen duniya sun yi jerin alkawari na rage dattin hayakin da ake fitarwa a lokacin taro kan sauyin yanayi a birnin Paris.

Sun bayyana fatansu cewa tattaunawar makonni biyun da za'a kwashe ana yi a Paris zai samar da sabuwar yarjejeniyar da za ta rage dumamar yanayi.

Manyan kasashen da tattalin arzikin su ke bunkasa, dama kuma masu karfin tattalin arziki sun bayyana yin aiki tare domin shawo kan bambance-bambance a kan girman matsalar da kudadan da za a kashe kan kowa ce irin yarjejeniya.

Koda a ce kasashen sun cika alkawuransu na rage datttin hayakin, masu fafutuka na shakkun cewa za su iya tsayar da dumamar yanayi.

Masana sun ce idan har aka samu karuwar sama da digiri biyu a ma'aunin celshiyos, zai iya haifar da wani bala'i a duniya, kamar tumbatsar teku da yanayi mai tsananin da kuma fari.