Rashin lantarki na kassara kasuwanci a Zambiya

Stanford Mwanza wanda ke aikin kafinta ya ce rashin wutar lantarki ya shafi kasuwanci nasa matuka.

Asalin hoton, james jeffery

Bayanan hoto, Stanford Mwanza wanda ke aikin kafinta ya ce rashin wutar lantarki ya shafi kasuwanci nasa matuka.

Bayan an dauke wutar lantarki da tsakar rana a garin Bauleni da ke birnin Lusaka, Stanford Mwanza mai shekaru 52, ya ci gaba da gudanar da sauran ayyukan sa na aikin kafinta inda ya mayar da hankalin sa wurin yin fenti.

Masu jiran wutar ta dawo na da dama a cikin garin Bauleni, inda cikin al'umma 15,000 da suka hada da masu aikin walda da kanikanci da masu sanya iskar tayoyin ababan hawa da sauran su.

Yawanci mutane na tayar da janarato lokacin rashin wuta.

Asalin hoton, james jeffery

Bayanan hoto, Yawanci mutane na tayar da janarato lokacin rashin wuta.

Daukacin al'umma miliyan 1.4 da ke Lusaka, babban birnin na Zambiya, wacce ke amfani da hanyoyin madatsun ruwa wurin samar da wutar lantarki, suna fama da matsalar karancin wuta, bayan halin rashin ruwa da suka shiga tsakanin watannin Oktobar bara da na Maris din bana, wanda ya mayar da madatsun ruwan kasa, kuma yayi sanadiyyar rashin wuta na sa'o'i takwas zuwa 14 a rana.

Zambiya na daya daga cikin kasashen Afrika da ta fi samun bunkasar tattalin arziki, inda cikin shekaru biyar, tattalin arzikin ke karuwa da kashi 7 cikin dari a duk shekara sakamakon inganta hakkar ma'adanan farin karfe watau Copper da kuma Cobalt da kasar ke yi.

Masu sukar gwamnatin na Zambia sun ce Ma'aikatar kula da wutar lantarkin kasar na bukatar sauyi.

Asalin hoton, james jeffrey

Bayanan hoto, Masu sukar gwamnatin na Zambia sun ce Ma'aikatar kula da wutar lantarkin kasar na bukatar sauyi.

'Rashin iya tafiyar da lamura'

Evans Chisokwe wani manomi a Bauleni ya ce, "Ya kamata shugabannin sun shiryawa wadannan matsaloli tun farko, yanzu ga shi yara ba su iya yin karatu da daddare."

Fiye da rabin wutar da Zambiya ke samu na zuwa ne daga madatsar Kariba Dam, wadda ke rafin Zambezi da ke tsakanin Zambiya da Zimbabwe, kuma mafi girman madatsar ruwan da dan adama ya kera.

Niels Bojsen, wani dan kasar Holland da ya hada gwiwa da wani kamfanin hannun jari da ke Lusaka babban birnin kasar, ya ce "Halin da Zambiya ke ciki shi ne manuni ga halin da sauran kasashen Afrika ke fama da shi wurin gudanar da kasuwanci."

Ya kara da cewa, "Tsirarun kasashe ke cikin kasashen goma da ke da ci gaban tattalin arziki, amma nan da nan sun shiga daya daga cikin kasashen da ke da yawan faduwar darajar kudi.

Mista Bojsen ya ce an fi samun mafita idan matsaloli irin haka suka afku a Turai, amma a kasa irin Zambiya, ba a san yaushe za a iya shawo kan matsalar ba.

Wani dan tasi da yaron sa suna safara man gyada domin samun karin kudin kashewa.

Asalin hoton, james jeffery

Bayanan hoto, Wani dan tasi da yaron sa suna safara man gyada domin samun karin kudin kashewa.

Tattalin arzikin Zambiya zai shiga matsanancin hali shekaru biyu nan gaba, amma arzikin ma'adanai da kuma alamun iya harkokin noma da kiwon kifi da kasar ke da shi za su farfado da shi.