Tambayar da ta gagari kimiyya? Me ya sa muke hamma?

Daga dama Shugaba Obama ne yake hamma
Bayanan hoto,

Daga dama Shugaba Obama ne yake hamma

Tun sama da shekaru 200 hamma ta gagari masana kimiyya gano sirrinta. To ko wani sabon nazari da aka yi zai kawo karshen wannan fafutuka ta amsa tambayar kowa ya huta? David Robson ya bincika.

Muna tsakiyar tattaunawa da Robert Provine, sai kawai na ji wani irin yunkuri daga cikina.

Ina kokarin dannewa amma ina sai kara karfi iskar take, tana tunkaro waje, ta bakina har sai da naji ta mamaye ni gaba daya, ta bude min baki ta fice da karfi.

A karshe dai abin kawai da nake tunani shi ne wai ta ya zan kare kaina daga hamma?

Provine ya gaya min cewa abu ne da ya saba faruwa idan mutane suna masa magana, lokacin gabatar da wata kasida, sai ya ga a wasu lokuta yawancin mutanen da suka taru a wurin suna wage baki (hamma).

Sa'ar da aka yi ita ce a matsayinsa na masani kan halayyar dan adam a Jami'ar Maryland da ke baltimore kuma marubucin wani littafi na halayyar dan-adam mai suna Curious Behaviour: Hamma da Dariya da Shakuwa da makamantansu abin ba ya damunsa.

''Hakan ya ma sa laccar ta fi armashi,'' ya ce. ''Kana magana sai mutane kawai su fara hamma.To ka ga daga nan sai ka sa mutane su fara gwaji a kan hammarsu, kamar rufe lebbansu ko su datse hakoransu ko kuma su matse hancinsu lokacin da suke hammar.''

Shugaba Putin na Rasha yana hamma

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Shugaba Putin na Rasha yana hamma

Da irin wadannan gwaje-gwaje ne Provine, ya yi kokarin bincika yadda abin da ya gagari masana kimiyya daruruwan shekaru wato Me ya sa muke hamma?

Dukkanmu mun san cewa gajiya da wahala ko kuma ganin wani duk suna sa mu hamma, to amma abin tambayar shi ne menene amfaninta ga jiki?

Lokacin da ya fara rubutu a kan hamma a wuraren karshen shekarun 1980 Provine ya rubuta cewa, ''hamma na iya kaurin sunan cewa ita ce abar da ba a fahimta ba sosai daga cikin dabi'un dan-adam.''

Kusan shekaru 30 bayan wannan magana tasa watakila mun kusa samun amsa, sai dai kuma kash, maimakon ta kawo karshen lamarin sai ta raba binciken.

wasu na ganin mutumin da ya fara nazari a kan hamma shi ne masanin nan dan kasar Girka Hippocrates kusan shekara 2,500 da ta wuce.

Shi yana ganin hamma tana taimakawa ne wajen fitar da gurbatacciyar iska ne daga cikin mutum, musamman lokacin zazzabi.

''Kamar tururin da ke fita idan ana dafa ruwa ne, iskar da ta taru a cikin mutum sai ta fice da karfi idan zafi ko dimin jikin mutum ya karu,'' kamar yadda ya rubuta.

An yi ta samun bayanai da fassara daban-daban a game da dalilin yin hammar har zuwa karni na 19, wanda a lokacin masana kimiyya maimakon su cigaba da kokarin lalubo dalilin da mutum yake yinta, sai suka karkata wajen cewa tana taimakawa wajen numfashi ne (wato amfaninta).

Inda take sa iskar da mutum ke bukata wajen numfashi (oxygen) ta gaggauta shiga cikin jini yayin da take fitar da iskar da mutum ke fitarwa ta numfashi, mai dumi (carbon dioxide).

To idan haka gaskiya ne, za ka sa ran mutane su rika hamma a kai a kai daidai da yawan iskar da mutane ke shaka ko kuma wadda suke fitarwa a iskar wurin da suke.

To amma abin ba haka yake ba, domin lokacin da Provine ya bukaci mutanen da yake nazari ko gwaji da su, su shaki wani gaurayen nau'in iska daban-daban bai ga wannan sauyi ba.

Harwayau masu nazari da dama kuma sai suka karkatar da bincikensu ya koma kan wani bangare na daban na hammar kuma, na yadda take yaduwa.

Wanda wannan kuma wani abu ne da ni kaina ban taba lura da shi ba sai a sanadin tattaunawata da Provine.

''Kusan kashi 50 cikin dari na mutanen da suka ga wani yana hamma su ma sai ta kama su'' in ji shi.

Hamma wata shu'umar aba ce mai karfin yaduwa ko tasiri a tsakanin mutane domin duk wani abu da ya shafe ta ya kan iya jawo ta.

Kamar ganin wani yana yinta ko jin wani ya yi, ko kuma ma karanta wani abu a kanta.''

A bisa wannan dalilin ne kuma wasu masu binciken ke ganin ko ma za ta iya kasancewa wata hanya ta sadarwa ta lokacin jahiliyya.

A nan kuma sai aka ce idan haka ne to wace sadarwa ce ake yi?

Yawanci idan muna hamma mun gaji ne, saboda haka sai wasu suke ganin tana taimakawa ne wajen saita ayyukan jikin mutum su zama daidai.

''Ni a fahimtata hamma za ta iya kasancewa wata hanya ce ta daidaita dabi'a ko halayyar mutane domin su je su yi barci, akalla a lokaci daya. Ma'ana tare,'' in ji Christian Hess na Jami'ar Bern ta Switzerland.

Ta wannan hanya da mutane ke barci tare kuma su tashi tare, tarinsu za su iya aiki tare yadda ya kamata a duk tsawon rana.

Haka kuma mukan yi hamma a lokacin wata damuwa: 'yan gasar tseren Olimfiks (Olympics) yawanci sukan yi hamma kafin tseren, yayin da masu kida da wake-wake su ma sukan yi kafin su fara yi a taro.

Saboda haka ne masana irin su Provine suka yi amanna, wannan kai-kawo da kake yi a lokacin da wani abu yake gabanka na damuwa zai iya kasancewa hanya ce ta sa kwakwalwarka ta sake shiri ta hanyar sa ka hamma, domin tunkarar kalubalen da ke gabanka.

Domin idan ka duba za ka ga a lokacin idan barci kake ji za ka wartsake ko kuma idan hankalinka yana wani wuri zai dawo ka natsu.

Idan hamma ta ratsa wasu tarin mutane za ka ga ta sa kowa ya mayar da hankali wuri daya, idan wata barazana ce a gabansu sai ka ga sun fuskance ta tare.

Ko da yake dai babu cikakken bayani dalla-dalla a kan wannan fahimtar amma wani mai bincike na Faransa Olivier Walusinki yana ganin hamma tana taimakawa wajen tura ruwan cikin lakar mutum zuwa kewayen kwakwalwarsa wanda hakan ke sa nan da nan a samu sauyi a aikin jikin mutum wato kamar yadda yake dawowa ya natsu ke nan idan yayi hammar.

Saboda tarin bayanan da ake da su, wasu masu rikitarwa wasu masu sarkakiya da kuma masu gogayya da juna, za a iya cewa samun wani bayani mai gamsarwa sosai a kan hamma yanzu dai ba a nan kusa ba.

To amma a 'yan shekarun da suka gabata an samu wani bayani da ya bullo, wanda ake ganin zai iya share duk tarin bayanan da suka gabata a lokaci daya.

Al'amarin hamma ya fara daukar hankalin Andrew Gallup, wanda yanzu yake Jami'ar Jihar New York a Oneonta, a lokacin da yake karatunsa na digirin farko, lokacin da ya fahimci cewa watakila hamma na taimakawa ne wajen sanyaya kwakwalwa domin ka da ta yi zafi sosai (misali kamar aikin lagireto a mota).

Yadda mukamukin mutum din nan yake motsawa da karfi kuwa ya ce hakan ne ke sa ya tura jini kewayen kokon kan mutum, domin ya taimaka wajen debe zafin da ya karu a kwakwalwa,wanda yake neman sa kwakwalwar ta tafasa, yayin da ita kuma iska mai sanyi (Oxygen) da mutum yake shaka ta shiga bakinsa lokacin da yake rufe bakin, ita ke komawa kwakwalwar.

Shi kuma motsi ko mikar da mutum yake yi a wannan lokacin da yake hammar na iya taimakawa ne wajen tayar da jijiyoyin yankin kan mutum ta yadda za su hura iska mai sanyi da za ta sa majinarmu da ke yankin kai fita kamar tururi, wanda hakan zai sa kanmu ya yi sanyi kamar na'urar sanyaya iska ( air conditioning).

A nan jarrabar da za a iya yi ta wannan fahimta ita ce, a duba a ga ko mutane za su fi yin hamma ko ba za su yi ba sosai a yanayi na sanyi da zafi daban-daban.

A yanayi da mutane suka saba kasancewa, Gallup, ya ga kusan kashi 48 cikin dari na mutane sun ji yanayin yin hammar.

Amma kuma da ya sa su kara wani abu mai sanyi a goshinsu, kashi tara ne cikin dari kawai suka ji hammar.

Da ya sa mutanen su rika numfashi ta hanci kawai, wanda shi ma hakan zai iya sanyaya kwakwalwa, sai tasirin ya fi bayyana, mutanen ba su ji wata hamma ba kuma.

Ka ga kenan a takaice wannan wata hanya ce ta kare yin hamma, inda duk wanda hamma ke neman ba shi kunya yayin wata tattaunawa mai gajiwarwa zai iya yin haka.

Hamma za ta iya zaburar da kwakwalwarka?

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Hamma za ta iya zaburar da kwakwalwarka?

Watakila shedar da ta fi dacewa a nan ita ce ta wasu mata biyu da hamma ta sa su gaba, wadanda suka je wajen Gallup, lokacin da ya bayyana sakamakon bincikensa.

Dukkanin matan suna neman yadda za a yi musu maganin cutar hamma ne yadda a wani lokaci sai su yi sa'a daya suna ta yin hammar.

Gallup ya ce, ''wannan na matukar takura musu a duk wani aiki kama daga na gida har zuwa na ofis har da mu'amullarsu ta yau da kullum.''

Hanyar da daya daga cikin matan take maganin larurar idan ta taso mata ita ce, ta yin wanka da ruwan sanyi.

Wannan ya karfafa wa Gallup gwiwa, inda ya bukaci matan da su sa dan ma'aunin sanyi da zafi a bakinsu kafin hammar ta taso musu da kuma bayan sun yi fama da ita.

Zatonsa ya tabbata, domin ya ga karuwar yawan zafin gab da lokacin da hammar za ta taso musu kuma zafin ya ci gaba da karuwa har ya kai lamba 37 a ma'aunin Selshiyas (37C).

Kuma wani abu mai muhimmanci dangane da wannan bayani ko fahimta na cewa hamma hanya ce ta sanyaya kwakwalwa, za a iya gane wasu daga cikin ayyukan jikinmu masu sarkakiya da suke sa mu hamma.

Za mu ga lalle dimi ko zafin jikinmu yana karuwa a ka'ida kafin da kuma bayan barci. Wanda kuma za ka ga idan ka sanyaya kwakwalwarka a hankali za ka iya wartsakewa daga barcin nan.

Sannan kuma kamar yadda bayani ya kasance a can baya, idan mutane suka kama hamma daga wannan zuwa wancan, za ka ga dukkanin taron mutanen sun wartsake, wato ta taimaka musu sun mayar da hankalinsu wuri daya.

Wannan hoton zai sa ka hamma?

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Wannan hoton zai sa ka hamma?

Wannan nazari ko bincike na Gallup ya gamu da tantama a wurin masu bincike kan hamma.

''Su Gallup ba su bayar da wata sheda ta gwajin da za a yi ba daki-daki da zai tabbatar da sheda ko mara baya ga nazariyyar ko matsayarsu ba,'' in ji Hess.

Masu sukan nazarin na Gallup musamman sun nuna cewa ai bai yi wani gwaji na gano hawa da saukar dumi ko zafi ko kuma sauyin zafin kwakwalwar mutane ba.

Amma shi kuma ya ce, ai ya yi wannan gwaji a kan wasu beraye da ke hamma.

Provine kuwa shi bai ja ko nuna shakku ga nazarin na Gallup ba. Hasali ma shi cewa ya yi, yana ganin hakan (bayanin na Gallup) wata hanya ce da hamma ke sa kwakwalwa ta dawo ta natsuwa wuri daya.

To dai ko da a karshe Gallup ya tabbatar da gaskiyar wannan bayani ko nazari nasa akwai sauran rina a kaba.

Wato akwai tarin abubuwa masu sarkakiya da suka shafi hamma, da ba a san dalilinsu ba. Misali daya a nan shi ne, me ya sa dan tayi (foetus) da ke cikin ciki yake hamma?

Watakila zai iya kasancewa dan tayi yana hammar ne a matsayin atisaye ko koyon yadda rayuwa za ta kasance masa idan ya fito duniya.

Ko kuma a ce hamma na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar jikin dan tayin, ta wurin taimakawa mukamukinsa ya iya motsawa ko kuma taimakawa girman huhunsa, in ji Provine.

To idan haka ne, Provine yana ganin amfanin hamma a ciki (dan tayi) ya fi tamu manya.

Haka kuma Provine yana ganin hamma da wasu abubuwan da jikin mutum ke yi kamar atishawa suna da kamanni ta wasu wurare da jima'i.

Ya ce idan ka duba za ka ga yanayin fuskar mutum duk daya ne idan yana cikin wadannan abubuwan.

Duba wannan hoton za ka fahimci maganar Provine

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Duba wannan hoton za ka fahimci maganar Provine

Jima'i, shi ma kamar hamma da atishawa na farowa ne a hankali a hankali sai ya yi karfin da ya fi mutum ko wani abu ya tsayar da shi idan ya kawo karshe, har ya kammala da wata gamsarwa wadda ba ta iya misaltuwa.

''Misali ai za ka ga a duk lokacin da hamma ko atishawa ta taso maka ba za ka iya hana ta kammaluwa ba, ko kuma a ce wani mutum ya katse maka su ba.'' Wannan shi ne yadda Provine ya dauka.

A karshe dai, ni ma hamma ta mamaye ni a lokacin wannan tattaunawa da Provine.

Zan iya tunawa rana ce mai dumi, ta lokacin bazara saboda haka ina ganin hammar da nake ta yi a lokacin tana hana kwakwalwata ne zafi a yayin wannan doguwar hira mai ban sha'awa da ilmantarwa.

Na tabbata kamar yadda Farfesa Robert Provine, ya ce, karatu ko tunani akan hamma, ko ma dai duk wani abu da ya shafi hamma, yana sa mutum ya yi ta.

Abu ne mai wuyar gaske a ce kai mai karatu kamar ni da na rubuta da wanda watakila ya fassara ba ku yi hamma daya ko biyu ko ma sau shurin masaki ba i zuwa yanzu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. One of science's most baffling questions? Why we yawn