Jonathan da Buhari sun yi kira a zauna lafiya

Zaben bana zai yi zafi sosai

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Zaben bana zai yi zafi sosai

Manyan 'yan takarar shugabancin kasa a Nigeria sun jadadda bukatar a samu zaman lafiya a lokacin zaben da za a gudanar a ranar Asabar.

A sanarwar hadin gwiwa, Shugaba Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari sun yi kira ga magoya bayansu da su kwantar da hankali kuma su yi zabe cikin tsanaki.

'Yan takarar sun fitar da sanarwar ce bayan tattaunawa da kwamitin da ke sa ido wajen tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a kasar.

Kwamitin ya na karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soji na Nigeria, Janar Abdussalami Abubakar da kuma Rabaran Mathew Hassan Kukah.

A ranar Alhamis ne ake kamalla yakin neman zaben da 'yan takarar shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki za su yi.

Tuni aka sanarda rufe kan iyakokin Nigeria a wani matakin tabbatar da tsaro da lafiyar 'yan kasar a lokacin zaben.