Ebola ta fi kashe kananan yara

Cutar Ebola ta hallaka mutane fiye da 10,000 da suka hada da yara da yawa a Afrika ta yamma

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Cutar Ebola ta hallaka mutane fiye da 10,000 da suka hada da yara da yawa a Afrika ta yamma

Wani bincike da mujallar New England ta gudanar ya yi hasashen cewa cutar Ebola ta fi muni tare da kashe yara kanana fiye da manya.

Masana kimiyya sun gano cewa cutar ta hallaka kashi 90 cikin 100 na jarirai 'yan kasa da shekara daya da suka kamu, idan aka hada da kashi 65 cikin 100 na manya da cutar ta kama a Guinea da Liberiya da Saliyo.

Duk da cewa yara kananan ba kasafai suke kamuwa da cutar ba, sai dai masu bincike sun ce akwai bukatar ganin cewa a samar masu da kulawa ta musamman.

Haka kuma an soma gwajin wata alurar rigakafi kan wasu mutane a Guinea.

'Kwayoyin halitta'

Cutar Ebola ta hallaka fiye da mutane 10,000 a kasashen Saliyo da Guinea da Liberiya a yammacin Afrika ta yamma inda cutar tafi kamari cikin watanni 12 da suka gabata.

Mafi yawan wadanda suka mutun dai manya ne, daya cikin mace-mace biyar ne kawai ake samun mutuwar yaro dan kasa da shekara 15.

Amma an samu yawan mutuwar yara kanana irin wanda ba a taba samu ba, tun bayan barkewar annobar ta wannan karon.

Jinyar mai cutar Ebola

Asalin hoton, bbc

Bayanan hoto, Jinyar mai cutar Ebola

Da aka fayyace bayanan da aka samu daga ma'aikatun lafiya na kasashen da abin ya shafa da kuma hukumar lafiya ta duniya WHO, masana kimiyya sun gano wani boyayyen al'amari na yadda mutane ke kamuwa da kwayar cutar dangane da banbancin shekarunsu ta hanyoyi daban-daban.

Bisa ga rahotannin da suka samar tun daga farkon barkewar annobar zuwa watan Janairun 2015, an tabbatar da cewa cutar ta kashe kashi 80 cikin 100 na yaran da suka kamu.

Kuma cutar tafi bunkasa nan da nan a jikin kananan yara, inda alamunta ke bayyana cikin sa'o'i 72 sabanin manya.

Farfesa Christ Donnelly na kwalejin Imperial da ke London, na daga cikin wadanda suka gudanar da binciken yace: "Yana da matukar muhimmanci mu samu hanyar magance wannan cuta ga yara da gaggawa."

"Muna kuma bukatar mu duba ko ana magance wannan cuta ga yara ta hanyar da ta dace da shekarunsu," in ji Farfesa Donnelly.

'Riga-kafi'

Har yanzu dai ba a samu wani magani da aka tabbatar da cewa zai warkar da cutar Ebola gaba daya ba.

Masana kimiyya a Guinea tare da hadin gwiwar hukumar kula da lafiyar al'umma ta Canada da kuma kamfanin Merck, suna aiki kan samar da riga-kafin da zai kare wadanda suke cikin hadarin kamuwa da cutar.

Dabarun sun hada da yin allurar riga-kafi da duk wani wanda ya yi mu'amala da mai dauke da cutar a baya-bayan nan don samar da ingantacciyar kariya.

Dakta Bertrand Draguez, na kungiyar likitocin agaji ta Medecins sans Frontieres, wanda shi ma yana daya daga cikin masu gabatar da gwajin, ya ce za a dinga aiwatar da gwajin akai-akai a kan mutane.

Sakamakon gwaje-gwajen zai samu daga a karshe watan Yuli.

Hukumar kula da lafiyar jama'a ta Ingila ma ta sanar da bayar da tallafin pam miliyan daya domin samar da wata hanyar murkushe cutar.