Jonathan ya yi kira a mutunta dokokin zabe

Jonathan ya bukaci 'yan Nigeria su zabi shugaban da ya kwanta musu a rai.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Jonathan ya bukaci 'yan Nigeria su zabi shugaban da ya kwanta musu a rai.

Shugaba Goodluck Jonathan ya yi kira ga 'yan Nigeria su mutunta dokokin zabe idan suka je kada kuri'unsu ranar Asabar.

Mr Jonathan, wanda ya bayyana hakan a jawabinsa na jajiberin ranar zabe, ya bukaci 'yan kasar su kada kuri'a cikin lumana, kuma su zabi shugaban da ya kwanta musu a rai.

Ya jaddada cewa miliyoyin 'yan kasar da a baya ba su samu katin zabe ba a yanzu sun karbin katunansu na kada kuri'a.

A ranar Alhamis, Mr Jonathan da dan takarar 'yan adawa, Muhammadu Buhari sun sha alwashin mutunta sakamakon zabe idan har an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.

Masu sharhi na kallon zaben a matsayin wanda ya fi zafi tun komawar kasar kan turbar mulkin demokuradiya a shekarar 1999.