Dabbobi ma na zaman makoki da jana'iza

Asalin hoton, AFP

Mun san cewa mutane sukan yi wasu abubuwa na jana'iza da makoki a kan mamatansu. To ga alama mu ma mutanen mun fara fahimtar cewa dabbobi ma suna jana'iza da makoki.

Jason Goldman ya yi mana nazari:

Idan Bayahude ya mutu, kamar yadda al'adarsu ta tanada wani daga cikin yahudawan da ake kira chevra kadisha zai zauna da gawar, inda zai yi ta mata karatu daga littafin Zabura har sai an binne ta.

Su kuwa mabiya darikar katolika na ddinin Kirista, abokai da iyalan mamacin ne za su zauna da gawar da daddare suna mata addu'o'i a abin da suke kira wake.

Asalin hoton, AP

Haka a zamanin da idan Rumawa suka mutu, nan da nan dangi za su kewaye gawar suna mata addu'oi.

Za a ajiye gawar a wani babban fili na kusa da gidan iyalan mamacin har zuwa lokacin da za a fara yi masa jana'iza.

Wadannan dabi'u ko al'adu kusan ana yinsu a sassa na duniya daban-daban.

Sai dai a ce sun bambanta daga wuri zuwa wuri ko daga al'umma ko kabila zuwa kabila.

Wasu mutanen suna ba da muhimmanci wajen ajiye ko duba gawar dan uwansu zuwa wani lokaci kafin su binne ta.

To amma kamar yadda muka fara fahimta wannan al'ada ba a cikin mutane kawai ta tsaya ba, ga alama tana nan a tsakanin dabbobi ma.

Asalin hoton, iony.head npl

A ranar 10 ga watan Oktoba na 2003, wani mai bincike ya ga yadda wata giwa mai suna Eleanor, wadda alamu suka nuna ba ta da lafiya, ta fadi.

Yanayin yadda jikinta yake kamar daman ta fadi kafin wannan lokaci domin har haurenta daya ya karye kuma hannunta (trunk) ya kumbura.

A wannan hali ne sai wata giwar mai suna Grace, wadda a wani garken daban take ta taho ta yi kokarin taimaka wa Eleanor ta tashi, tana amfani da haurenta domin ta daga ta, amma kafofin Eleanor na baya sun yi rauni matuka.

Ganin haka sai sauran giwayen na garken su Grace, suka ci gaba da tafiyarsu amma ita Grace ta tsaya a wurin Eleanor kusan sa'a daya har lokacin da almuru ya yi a Kenya.

Washegari da karfe 11 na safe Eleanor ta ce ga garinku nan, rai ya yi halinsa.

Asalin hoton, AFP

Tattaruwar da giwaye suka yi a wurin gawarta da kai-kawon da suka yi ta yi, abin da za ka iya kwatantawa ne da abin da wasu mutane suke yi lokacin da za a binne wani babban mutum da ya rasu, inda ake ajiye gawarsa kowa yana zuwa ya yi masa kallon karshe sannan, ya yi masa addu'a.

A cikin kwanakin nan da mutuwar wannan giwa sai da garke-garke na giwaye daban-daban har guda biyar suka rika zuwa suna ziyartar gawar ko mushen, kuma wasu daga cikinsu ma ba su da dangantaka da ita Eleanor din.

Haka kowace giwa za ta je kan gawar ta shinshina ta dan dungure ta tana taba ta da kafa da kuma toro.

Duk da cewa ungulaye da kuraye da sauran dabbobin daji sun zo sun ci rabonsu a jikinta kuma tana karkashin ikon zakuna a rana ta hudu, sauran giwaye sun ci gaba da kasancewa a wurin da ba shi da nisa sosai da mushen da rana.

Tun da dai ba dangin Eleanor ba ne kadai suka hallara a wurin gawarta har da wasu giwayen da ba su da dangantaka da ita da su ma suka zo tare da nuna abin da za a iya cewa

alhininsu (kamar yadda mutane ke yi ) a kan mutuwarta, masana kimiyya da suka ga yadda abin ya kasance, sai suka zartar cewa giwaye suna da al'ada ta nuna damuwa gaba daya a kan mamaci.

An samu shedar wannan dalili daga sauran bincike da aka gudanar.

Kuma duk da cewa dabi'ar da giwayen suka nuna ta bambanta da abin da mutane suke yi wa mamacinsu amma duk da haka abu ne na daban idan aka yi la'akari da dabi'ar giwaye.

Jana'iza da makoki a teku

Mutane da giwaye ba su kadai ba ne suke ziyartar gawar wani nasu da ya mutu ba dadewa.

Asalin hoton, z

A ranar shida ga watan Mayu na shekara ta 2000, an ga gawar wani kifi irin wanda ake kira dolphin da Ingilishi, a can karkashin teku, a wurin da ke da nisan mita 50 daga gabar gabas ta tsibirin Mikura a kusa da Japan.

An ga wasu kifayen irinsa maza kuma manya guda biyu sun rika kasancewa da gawar a ko da yaushe, sai dai su taso saman ruwa na dan lokaci su shaki iska sannan su koma.

Tun da ba a san dalilin mutuwar ba, masu linkaya sun yi kokarin su dauko gawar domin a yi bincike a kanta, amma wadannan kifayen biyu manya suka hana daukarta.

A rana ta biyu ma masu binciken sun sake komawa wurin domin daukar gawar ta macen kifin amma wadannan mazaje biyu suka hana.

A rana ta uku kuwa sai ba su ga gawar ba. Masu binciken suna ganin ruwa ya tafi da ita.

Wannan ba shi kadai ba ne nazarin da aka yi na wannan dabi'a kan mutuwar kifin wanda ake kira dolphin.

A ranar 20 ga watan Yuli na 2001, an ga gawar wani matsakaicin irin kifin a tsakanin wasu manyan duwatsu biyu a karkashin teku a wata gaba da ke kusa.

A kusa da gawar wasu sauran kifayen irinsa, maza da mata akalla su 20 sun yi dandazo.

Lokacin da masu linkaya suka yi yunkurin zuwa su dauki gawar sai gungu-gungu kusan daya zuwa uku na wasu maza daga cikin kifayen suka tayar da kayar baya, suna kokarin tare masu linkayar, ko da yake dai barazanar ta su a nan ta tsaya kawai.

Su ma wadannan kifaye kamar wadancan giwayen na Afrika, sun rika shinshina gawar dan uwan nasu suna taba ta da baki da kuma kansu, cikin damuwa da bakin ciki.

Bayan da a karshe masu linkayar suka samu damar dauko gawar kifin, da yawa daga cikin wadanda suka kewaye ta sun rika bin kwale-kwalen mutanen har sai da suka zo tasharsu ta jiragen ruwa.

Haka kuma lokacin da wasu masana kimiyya suka ga gawar wani dan karamin irin wannan kifi na dolphin a kusa da tsibiran Canary Islands, a watan Afrilu na 2001, su ma sun ga sauran irin kifin sun kewaye ta, suna ganin ma daya daga cikinsu uwarsa wanda ya mutun ce.

A rana ta uku da mutuwarsa sai gawar ta fara yawo a saman ruwa, kuma a rana ta hudu ta fara nuna alamun rubewa.

Duk da cewa masana kimiyyar ba su yi kokarin daukar gawar ba, amma sun lura cewa a duk lokacin da hatta tsuntsaye suka yi kokarin zuwa kusa da gawar wadda ke yawo a kan ruwa, nan da nan sai sauran kifayen su kore su.

Ganin cewa mutane na kusa tare da sanya ido a kan wadannan kifaye (dolphins) a lokacin da suke lura da gawar dan-uwan nasu, masu bincike suna da madogarar da za su iya cewa kifayen sun yi hakan ne saboda mutane suna kusa da su amma ba lalle haka dabi'arsu take ba.

A lokacin kifayen suna tafiya a hankali a hankali ne kuma sun dade a wuri daya fiye da yadda ake tsammani.

Duka wadannan abubuwa biyu za a iya cewa kifayen na yinsu ne domin mutuiwar nasu.

Hasali ma a duk wuraren biyu kifayen sun kewaye gawawwakin tare da kokarin hana zuwa kusa da su.

A duka biyun kifayen sun kama wani aiki daban da abin da suka saba yi na yau da kullum ( watakila saboda an yi musu mutuwa).

Sanin mutuwa

A wani bangaren kuma su birai suna cigaba da ayyukansu na yau da kullum duk da an yi musu mutuwa.

Sai dai a tasu dabi'ar uwar dan da ya mutu tana daukar gawar ne ta rika yawo da ita wurin harkokinta na yau da kullum har tsawon kwanaki a wani lokacin ma makwonni ko ma watanni.

Uwar tana cigaba da kula da gawar wanda hakan yake sa ba ta saurin rubewa.

Haka take yi da ita tsawon lokaci, inda ba za ta daina ba har sai ta ga gawar ta rube ba ta iya gane ta kuma.

Lokacin da wata 'yar biranya mai watanni uku ta mutu a gidan namun daji na LA, masu kula da gidan sun bar wa uwar mai suna Gracie ta ci gaba da rike gawar 'yar tata har tsawon kwanaki, domin ta yi wa gawar wannan makoki ko jana'iza da biran suka saba yi.

An yi cikakken bayani kan wannan al'adar makoki ta birai bayan da masu bincike a Zambia, suka yi sa'ar ganin wata biranya (matar biri) mai suna Masya wadda ke dauke da gawar wani jaririnta dan watanni hudu.

A rubutun da ta yi a mujallar abubuwan da suka shafi birirrika ta Amurka ( American Journal of Primatology), wata mai bincike, Katherine Cronin, ta ce ita tana ganin:

''Halaye da abubuwan da wannan tamatar biri ta yi lokacin da take cikin bakin cikin mutuwar dan nata sun bayar da haske sosai a kan watakila hanyoyin da biri yake sanin rai ko mutuwar wadanda suke tare da shi.''

Masu bincike sun ga sauran birirrika iri daban-daban su ma suna wannan dabi'a.

Giwaye da kifaye (nau'in dolphins) da kuma birirrika, dukkaninsu suna da halaye da dabi'u masu wuyar fahimta wadanda kadan daga ciki za mu iya sani ko ganewa.

Saboda haka abu ne mai wuya a ce mun iya lura da yadda suke yi idan an yi musu mutuwa a daji, inda suke rayuwa ba tare da ganin wata halitta kamar mutum ba tana kusa da su, ballantana su yi wani abu daban, illa dabbobi 'yan uwansu.

A don haka yawancin wadannan bayanai da muka yi an same su ba ta wata hanyar gwaji na sosai ba.

Amma duk da haka, sheda ta nuna mutum ba shi kadai ba ne dabba ko halittar da ke da wata al'ada ta daban a kan mamacinsa.

Kuma yawan dabbobin da ake ganin suna da wannan al'ada ta yi wa mamatansu makoki ko jana'iza na ci gaba da karuwa.

Saboda wasu rahotanni da aka samu a 'yan shekarun nan sun nuna alamun cewa rakumin-dawa da wata tsuntsuwa nau'in benu (western scrub), su ma kamar suna da yadda suke makokin 'yan uwansu da suka mutu.

Mu mutane muna son mu yaudari kanmu ko mu dauka cewa mu wasu halittu ne na daban ko na musamman a cikin dabbobi.

Ko da ike haka ne ta wani bangaren, mu na daban ne. To amma mu san cewa fa ko da akwai wata dabi'a da mu kadai muke da ita, akwai kuma wasu dabi'un daruruwa da muka yi tarayya a kansu da sauran dabbobi.

Don gudun nuna wa sauran dabbobi irin yadda muke fifita kanmu a kansu, ya kamata mu rika tunawa cewa, mu ma kanmu fa dabbobi ne ta wata hanyar.

Anya ma duk wannan magana da muke yi ba ihu ba ne bayan hari, ganin yadda muka dage wajen sai mun bayyana wata dabi'a da muke gani tamu ce, alhali ma abu ne da yake zaman kamar halitta a tare da mu, halittar da ba mu ne muka kirkireta ba, kawai mun wayi gari ne muka ga muna yinta?

Mai aikin kintsa gawar mutumin da ya mutu ba dadewa, wanda yake sanya wa gawar wasu sinadarai domin ka da ta yi wari ko ta rube da wuri, da zai lura sosai, zai ga cewa akwai kamanceceniya fiye da yadda watakila ya sani da uwar dan birin da ya mutu, wadda take ta yawo da gawar, tana ciccire kwari daga gawar, wanda hakan ke hanata rubewa da wuri.

A nan abin da ya kulla dangantakarmu da biri, shi ne dukkanninmu muna kokarin mu san yadda mutuwa take ne amma ta hanyoyi daban-daban.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan <link type="page"><caption> Death rituals in the animal kingdom.</caption><url href="http://www.bbc.com/future/story/20120919-respect-the-dead" platform="highweb"/></link>