Fiye da mutane 4300 ne suka mutu a Nepal

Masu aikin ceto a Nepal

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu aikin ceto a Nepal

Hukumomin kasar Nepal sun ce kawo yanzu, fiye da mutane dubu 4300 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon bala'in girgizar kasar da ya afkawa kasar ranar Asabar.

Wasu mutanen kimanin dubu takwas kuma sun samu raunuka.

Ana ci gaba da aikin ceto ko da za a samu wasu da ransu, sai dai har yanzu ba a fara aikin ceton a wasu yankuna ba.

Mutane da yawa a babban birnin kasar, Kathmandu sun kwana a waje a rana ta uku saboda fargabar da suke yi bayan kananan girgizar kasa da aka samu ranar Lahadi.

Gwamnatin kasar ta ce tana bukatar abubuwa da yawa da suka hada da barguna da jirage masu saukar ungulu da kuma likitoci da direbobi.

Akwai karancin ruwan sha da abinci da kuma wutar lantarki, sannan ana fargabar barkewar cututtuka.