Ana yin addu'oi a kan harin Paris

Shugaba Francoise Hollonde

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Francoise Hollonde

A ranar Juma'a ne ake gudanar da addu'oi domin tunawa da mutane 130 da suka mutu sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Paris makonni biyu da suka gabata.

Shugaba Francoise Hollande ne dai zai jagoranci taron a wani katafaren filin taro da ke tsakiyar birnin na Paris wanda gidan tarihin sojoji yake ciki.

Ana sa ran kimanin mutane dubu daya za su halarci taron, cikinsu har da shugaba Faransa da shugabbanin siyasa da mutanen da suka tsira daga harin da kuma iyalan mutanen da aka kashe.

Za a yi shiru na minti guda sannan za a kira sunayen dukkanin mutanen da aka kashe.