An kara ceto mutane 20 daga Sambisa

Sojin Najeriya na ci gaba da ceto mutane daga dajin Sambisa
Bayanan hoto, Sojin Najeriya na ci gaba da ceto mutane daga dajin Sambisa

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kara ceto yara da mata kimanin 20 daga dajin Sambisa a hare-haren da take ci gaba da kai wa mayakan kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce sojojinta na ci gaba da kutsawa cikin dajin Sambisa, inda suka kai hare-haren da ya yi sanadiyar mutuwar mayakan Boko Haram da dama a ranar Juma'a.

An lalata makaman mayakan Boko Haram din da dama da manyan tankokin yaki da babura 70 da kuma motoci bayan arangamar da suka yi da sojojin.

Kazalika kimanin sojoji 10 ne suka samu raunuka yayin da soja daya ya mutu sakamakon tashin bama-baman da 'yan kungiyar suka binne a hanyar da sojojin suka wuce.

Kimanin watanni biyu ke nan da rundunar sojin Najeriya ta fara kai hare-hare a kan sansanonin Boko Haram da ke dajin Sambisa, inda suka ceto dumbin mutane.