Barca ta yi korafi kan masu sharhin wasanni

Barcelona ce ta doke Real Madrid da ci 4-0 a Bernabeu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Barcelona ce ta doke Real Madrid da ci 4-0 a Bernabeu

Barcelona ta shigar da korafi kan tsoffin 'yan wasan Real Madrid, saboda jawabin da suka yi cewar a yi wa Neymar keta a lokacin da suke sharhin wasan El Clasico.

A karawar da Barcelona ta doke Real Madrid 4-0 a Bernabeu, sai da aka bai wa Isco jan kati saboda ketar da ya yi wa Neymar daf da za a tashi daga fafatawar.

Barca ta ce Manolo Sanchis da Poli Rincon sun yi ta yayata cewar ya wajaba da a jikkata Neymar da harshen Spaniyanci a lokacin da suke sharhin wasan a Radiyo.

Kungiyar ta tuntubi gwamnatin Spaniya domin a kawar da tayar da tarzoma a lokacin wasan kwallon kafa.

Barcelona ta ce jawaban da masharhantan wasan suka yi za su iya tayar da tarzoma a filin, saboda haka tana son a dauki matakin ladabtarwa a kansu.

Barca na zargin Sanchis da cewa "Neymar yana wuce gona da iri, kuma ba a yi masa kyakkyawan duka ba", shi kuwa Rincon an zarge shi da furta cewar "Idan da ina wasan da tuni na make shi".