Masu kallo suna so mu rika yin rawa — Rahma Sadau

Rahma Sadau na daya daga cikin matan da suka fi haskakawa a fina-finan Kannywood.

Asalin hoton, Rahma Sadau

Bayanan hoto, Rahma Sadau na daya daga cikin matan da suka fi haskakawa a fina-finan Kannywood.

Jarumar fina-finan Hausa, Rahma Sadau, ta ce masu kallon su sun fi sha'awar fina-finan da ake yin raye-raye da wake-wake.

Rahma ta shaida wa BBC cewa sun gano haka ne sakamakon tambayoyin da suke yi wa masu kallon fina finan na Hausa, wadanda aka fi sani da Kannywood.

A cewar ta,"Idan na ce zan yi Film din Hausa na saka kalangu; ba za a kalla ba. Ka san da haka ko? Saboda komai akwai lokacin sa. Amma idan aka ga Rahma na rawa, cewa za a yi je ka ka nemi Film din. Me ya sa ake yin haka? Ana yi ne saboda muna yi wa mutane abin da suke so. Wani lokacin ba ma yin Film sai mun tambayi mutane abin da suke so su kalla".

Ta ce fina-finan Indiya sun yi tasiri sosai kan fina-finan Hausa ne saboda yawanci al'adu da dabi'un Hausawa sun yi kama da na Indiya.

Sai dai ta kara da cewa hakan ba zai sa su daina yin fina-finan da ke fito da al'adu da dabi'un Hausawa na asali ba.

Ta jaddada cewa ta fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya, wato Nollywood ne domin taka rawa ta "musamman".

A cewar ta, ba za ta yi duk wani abu da zai tozarta addini da al'adunta ba.