Ta yaya za a yi maganin Kungiyar IS a Iraki?

Rigar wani soja ne yashe kasa gaban wata motar sojojin da aka kona kusa da Mosul, a watan Yuni 2014.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rigar wani soja ne yashe kasa gaban wata motar sojojin da aka kona kusa da Mosul, a watan Yuni 2014.

A ranar Lahadi ne, a garin Ramadi a Iraki mai tazarar mil 70 tsakanin ta Bagadaza ya koma karkashin ikon kungiyar IS.

'Yan sanda da sojoji sun tsere, bayan an yi kwanaki ana fafatawa, har kuma an nuno bidiyo da ke nuno motocin yaki na tserewa cikin hanzari, yayinda kungiyar IS tayi ikirarin kama tankunan yaki da makamai masu linzami da dakarun suka bari a baya.

A watan Yunin shekara ta 2014, makamancin haka ya faru lokacin da IS ta kwace garin Mosul, wanda shi ne babban birnin Iraki na biyu da kuma Fallujah a watan Junairu 2014 da kuma Tikrit a watan Yuni 2014, duk da cewa sojojin sun sake kwato Tikrit yanzu.

Menene dalilin gazawar sojojin gwamnatin Iraki a yaki da IS, kuma waye zai iya da su ? Ana tunanin watakila mayakan Shi'a su yi nasara inda sojojin Iraki ta gaza.

'Cin hanci da rashawa'

Wasu 'yan kungiyar IS rike da tutarsu suna yawon gadi cikin motar sojoji, a wani yankin Iraki Fallujah, a watan Maris 2014.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, Wasu 'yan kungiyar IS rike da tutarsu suna yawon gadi cikin motar sojoji, a wani yankin Iraki Fallujah, a watan Maris 2014.

A shekarar 2014, wata kungiya da ake kira 'International Strategic Studies Groups' ta rubuta yawan dakarun sojin Iraki sun kai 193,000, kuma watakila 'yan sanda da masu kwantar da tarzoma sun kai 500,000.

Hukumar leken asiri ta Amurka ta na ganin mayakan kungiyar IS sun kai 31,000 a Iraki da Syria, saboda haka ya kamata sojojin gwamnatin su samu galiba a kan su, idan da gaske haka kidayar ta ke a kasa.

Bincike da aka yi kan cin hanci da rashawa a tsakanin sojin Iraki a watan Nuwanba 2014, ya nuna cewa akwai sunayen bogi 50,000 da ake biyan albashi a tsakanin sojojin.

A tsakanin sojojin an wa ire-iren wadannan mutane lakani da "fatalwan sojoji", ba a san da su ba kuma duk da cewa ana biyansu albashi.

'An kasa samun nutsuwa'

An rusa dakarun sojin Saddam Hussein gaba daya, aka meye gurbinsu da sojojin da ake kyautata zaton za su zama na kowa da kowa.

Amma ga dukkan alamu, an samu kura-kurai da dama.

Ana tunani an yi kuskure da aka tsayar da rundunar sojin da ta ke kwaikwayon tsarin nasara.

Janyewar da dakarun sojin Amurka suka yi a karshe 2011, ya kawo karshen horon sojin Iraki da suke sa wa ido, hakan kuma ya sa suka shiga wani halin rashin kwarewa a yaki.

A halin yanzu kuma dole ne yaba wa sojojin Saddam, domin su ne wadanda suka fi kwarewa a yaki.

'Mayakan Shi'a'

Mayakan Iraki mabiya akidar Shi'a Asaib Ahl al-Haq (dangin salihai) suna gadin hedikwatarsu a Basra.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mayakan Iraki mabiya akidar Shi'a Asaib Ahl al-Haq (dangin salihai) suna gadin hedikwatarsu a Basra.

A watan Yunin 2014, bayan an kwace Mosul, wasu mayakan sun kafa wani hadin gwiwa, da suka sa wa suna 'Popular Mobilization Force' wanda ya karfafa sosai, domin dakile barazanar kungiyar IS.

Wakilin BBC Murad Batal Shistani, ya ce hadin gwiwar ya ka su kungiyoyi biyu.

Wadanda suka kafa tushe da kungiyoyin kwantar da tarzoma, kamar Badr Birged da dakarun Hezbollah da Asaib Ahl al-Haq da sauran su.

Wasu rahotanni sun nuna akwai alaka tsakanin kasar Iran da wadannan kungiyoyin.

Kaso na biyu cikin kungiyoyin da aka kafa na Popular Mobilization Force, yana kunshe ne da mabiya akidar Shi'a, watau masu fatawar yaki da kungiyar IS.

Bayan 'yan kwanaki da kwace Mosul, Babban malamin 'yan Shi'an Iraki ya yi kira da a yi jihadi.

Rahotanni daga Bagadza na cewa matasa 'yan Shi'a na ta zuwa rajista a masallatai kuma suna zuwa horo a wasu sansanoni da aka kafa domin shirin yaki.

Wannan kungiya da aka kafa za ta iya dakile IS a Ramadi kuwa?

Mabiya Sunnah a garin Anbar sun shiga kungiyar Mobilization force - nasarar yakin kwato Ramadi ya danganta da halin mabiya akidar Sunnar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mabiya Sunnah a garin Anbar sun shiga kungiyar Mobilization force - nasarar yakin kwato Ramadi ya danganta da halin mabiya akidar Sunnar.

'Yan Anbar mabiya akidar Sunnah, sun shiga kungiyar 'Popular Mobilization force' din kuma nasarar kungiyar ta dangana da hadin kan 'yan sunna.

Kungiyar Mobilization force ta yi nasara a kan IS bayan ta kwato garin Tikrit, amma ana zargin su da yin "ramuwar gayya" a kan wasu 'yan sunna a wadannan yankunan.

Kakakin wani sashi na kungiyar Mobilisation force din Kataib Hezbollah a Iraki, Jaafar al-Hussein ya shaida wa BBC cewa duk da cewa wannan shi ne hadin gwiwar da ta fi karfi da sojojin Iraki, masu akidar sunni basu yarda da matsayin su ba.