An hana 'yan gudun hijirar Ramadi shiga Baghdad

Mayakan IS ne suka kwace birnin Ramadin

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mayakan IS ne suka kwace birnin Ramadin

Mataimakin shugaban mai kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya a Iraqi ya yi magana game da halinda mutanen da akai kiyasin 40,000 suke ciki , wadanda suka tserewa birnin Ramadi, birnin da ya fada hannun ikon mayakan IS kusan mako guda da ya wuce.

Dominik Bartsch ya fadawa BBC cewa mutane da dama da suka rasa matsugunansu da suka hada da mata da dattawa da kuma marasa lafiya sun makale a wata gada dake mashigar birnin Bagdad, inda aka hana su shiga birnin.

Ya ce akwai rahotannin da ke cewa wasu daga cikin kananan yaran cikinsu ma sun mutu saboda kishin ruwa.

Mr Bartsch ya ce majalisar dinkin duniya ta kuma damu game da sauran 'yan gudun hijirar da yaki tsakanin mayakan IS da dakarun gwamnati ya rutsa da su