An tsige mataimakin gwamnan Ondo

Wasu na ganin an tsige Alhaji Olanusi ne saboda ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Asalin hoton, media

Bayanan hoto, Wasu na ganin an tsige Alhaji Olanusi ne saboda ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Rahotanni daga jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa 'yan majalisar dokokin jihar sun tsige mataimakin gwamna, Alhaji Ali Olanusi.

Rahotanni sun ce an tsige Alhaji Olanusi bisa zargin yin amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba.

A cewar rahotannin, 'yan majalisa 24 daga cikin 26 ne suka tsige mataimakin gwamnan.

A kwanakin baya ne dai Alhaji Ali ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Masu sharhi na ganin cewa 'yan majalisar dokokin sun cire shi ne saboda sabanin da ke tsakaninsa da gwamnan jihar, Olusegun Mimiko, wanda ke matukar goyon bayan shugaban kasar Goodluck Jonathan.