"An yi cuwa-cuwa sosai a NNPC"

Nigeria ce kasar da ta fi kowacce hako danyen mai a Afrika
Bayanan hoto, Nigeria ce kasar da ta fi kowacce hako danyen mai a Afrika

Kamfanin da aka dora wa alhakin gudanar da bincike a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a kamfanin man fetur na Nigeria, NNPC ya ce ana cuwa-cuwa sosai wajen biyan kudaden tallafin man fetur da kalanzir.

Kamfanin PricewaterhouseCoopers ya ce a wasu lokutan NNPC na biyan kamfanoni kudin tallafin man fetur sau biyo.

Masu binciken sun ce akwai bukatar a yi wa dokar da ta kafa NNPC garanbawul domin tabbatar da cewa dukkanin kudaden da kasar ke samu daga sayar da danyen mai na shiga asusun gwamnatin tarayya kai-tsaye.

Rahoton na binciken kuma ya bukaci NNPC ya mayar wa gwamnatin Nigeria kusan dala biliyan daya da rabi saboda kin saka wasu kudaden da aka sayar da man fetur a kasar.

A bara ne gwamnatin shugaba Jonathan ta dauki hayar kamfanin PricewaterhouseCoopers domin bin diddigin zargin da tsohon gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi ya yi cewar an yi sama da fadi da kusan dala biliyan 20 na harajin danyen mai da kasar ta sayar.