Hoeness zai shafe shekaru uku a kurkuku

Shugaban Bayern Uli Hoeness
Bayanan hoto, Shugaban Bayern Uli Hoeness

An yanke wa shugaban kungiyar Bayern Munich na Jamus hukuncin daurin shekaru uku da rabi a gidan yari, bayan kotu ta same shi da laifin kin biyan haraji.

UIi Hoeness, wanda a lokacin kuriciyarsa yana daga cikin 'yan wasan da suka ciyo wa Jamus kofin kwallon kafa na duniya, ya amince ya aikata zamba sosai ta kin biyan haraji.

Ya yarda cewa, kamata yayi ya biya hukumomin harajin Jamus kudi Euro miliyan 27, bayan wata hada-hadar hannayen jarin da yayi, ta hanyar asusun ajiyarsa na banki a Switzerland.

Uli Hoeness dai yayi tayin yin murabus daga kungiyar Bayern Munich mai rike da kofin zakarun Turai.

To amma dole ya janye tayin, yana hawaye, lokacin da magoya bayan kungiyar suka yi ta masa kirari, su na ambaton sunansa.