Samsung: Babu matsala a hada-hadar kudinmu

Kamfanin Samsung mai latronik

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kamfanin Samsung mai latronik

Kamfanin Lataroni na Samsung ya ce tsarinsa na biyan kudi ta hanyar wayar salula bai da wata matsala bayan da wasu masu kutse ta intanet a Amurka suka yi wa LoopPay kutse.

Jaridar New York Times ta ce an yi kutsen ne a reshen Samsung mai suna LoopPay a watan Mayu.

Samsung ya sayi LoopPay a watan Fabarairu, wanda ke samar da tsarin biyan kudin da ake amfani da shi wajen gudanar da ayyukan Samsung Pay mai hammaya da tsarin Apple Pay.

Samsung ya ce wannan tsarin bashi da wani hadari.

A watan Agusta, baban kamfanin latroni na kasar Koriya watau, Korea Electronics shi ma ya kaddamar da tsarin biyan kudi ta wayar salula na Samsung pay din a Korea ta Kudu, sai kuma ya kaddamar da tsarin a Amurka a watan satumba.

Tsarin biyan kudi na Samsung pay na gasa da tsarin biyan kudi na Apple's pay, wanda aka kaddamar a bara kuma ana amfani da tsarin a Amurka da kuma Ingila.

Google ma da shigen tsarin biyan kudin na wayar salula.

Asalin hoton, Reuters

An samar da tsarin biyan kudi a wayar salula ne domin shawo kan masu sayyaya su yi amfani da wayoyin salula su yi sayayya mai makon yin amfani da kati.

'Lamuran da aka ware'

Jaridar New York Times ta bayyana a rahotanta cewar wasu 'yan kasar China wadanda ake kira kungiyar Codoso - sun samu damar yin kutse a kan kamfanin LoopPay kuma ba a gano su ba har sai bayan watanni biyar a cikin watan Agusta.

Samsung ya kara da cewar "babu wani tasirin da kutsen yayi a kan tsarin biyan kudinsa na salula kuma babu wani bayani na wani wanda ya ke cikin hadari."

Kamfanin ya ce abin da ya faru kebabbe ne kuma ya jadadda cewar tsarin biyan kudi na LoopPay wani reshe ne daban daga tsarin biyan kudi na Samsung Pay.

Asalin hoton, Samsung

"An warware lamarin tsarin biyan kudi na LoopPay kuma bai da wani alaka da tsarin biyan kudi na Samsung Pay, " in ji Kamfanin.

Ken Westin ma'aikacin kamfanin tsaro na Tripwire ya gayawa kamfanin Computer world cewar "Ba lallai bane, wadanda suka yi kutsen suna sha'awar satan bayanan da za su iya sayarwa ne".