Nigeria za ta yi shawagi da jirage a bakin iyaka

Ministan cikin gidan Najeriya, Abba Moro

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Kasar za kuma ta yi amfani da motoci wajen sintiri a bakin iyakokinta, tare da na'urori na zamani

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Najeriya ta ce hukumar kula da shige-da-fice ta fara amfani da jiragen sama wajen yin sintiri a kan iyakokin kasar.

Tuni dai ministan harkokin cikin gidan Najeriyar, Abba Moro ya umurci hukumar shige da ficen da ta hada hannu da wani kamfanin jiragen sama mai suna Donier domin gyara wasu jiragen saman hukumar da suka lalace.

Haka kuma hadin guiwar zai samar da wasu sababbin jirage domin cimma wannan manufa.

Najeriya dai na fuskantar kalubale wajen tsare kan iyakokinta, sakamakon matsalar bazuwar makamai da safarar miyagun kwayoyi da kuma kutsen masu tayar da kayar baya ta wasu iyakokinta.