Hukumar SSS ta tsare mai kamfanin 'Card Reader'

INEC ta gudanar zaben gwaji da na'urar 'Card Reader'

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto, INEC ta gudanar zaben gwaji da na'urar 'Card Reader'

Rahotanni daga Nigeria na cewa jami'an hukumar farin kaya ta SSS suna tsare da Alhaji Sani Musa, watau mai kamfanin da ya yi wa hukumar zaben kasar kwangilar samar da na'urar tantance masu kada kuri'a da aka sani da 'Card Reader'.

Bincike dai ya nuna jami'an hukumar farin kayan sun gayyace shi ne tun a ranar Talatar da ta wuce, inda daga nan suka ci gaba da tsare shi.

A ranar Laraba ne, daraktan yada labarai na gangamin yakin neman zabe na shugaba Goodluck Jonathan, Femi Fani Kayode a wata hira da manema labarai ya zargi shugaban kamfanin da ya yi kwangilar katin da cewar dan jam'iyyar adawa ta APC ne.

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria na adawa da amfani da 'Card Reader' a yayinda INEC ta ce hakan zai rage magudi a ranar zabe.

Jam'iyyar APC a nata bangaren, ta ce amfani da 'Card Reader' ne zai tabbatar an yi sahihin zabe a Nigeria.