An sanya dokar hana fita a Baltimore

'Yan sanda suna korar masu zanga zanga a Baltimore

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan sanda suna korar masu zanga zanga a Baltimore

An sanya dokar ta-baci da kuma dokar hana fita ta tsawon mako guda a birnin Baltimore na kasar Amurka domin kwantar da tarzomar da jama'a suke yi.

Wasu jami'an gwamnati sun ce tarzomar da ake yi ita ce mafi muni tun bayan wadda ta biyo bayan kisan Martin Luther King a shekarar 1968.

Magajiyar garin birnin Baltimore, Stephanie Rawlings Blake, ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana sace-sace da barnata kayayyaki da kuma kona gidaje da ake yi da sunan tarzoma.

Tarzomar ta taso ne bayan amutuwar Freddie Gray, wani Ba'Amurke bakin fata mai shekaru 25 da 'yan sanda suka yi wa mummunan rauni lokacin da suke tsare da shi.

Jami'an 'yan sanda sun ce masu zanga-zangar sun jejjefe su da duwatsu, da bulo da kuma kwalabe, lamarin da ya sa 'yan sanda 15 suka samu ranuka.