BH: 'Yan Sandan Nigeria za su karbi aikin tsaro

Rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta ce ta shirya tsaf, domin karbar aikin tabbatar da tsaro a yankin arewa-maso-gabashin kasar wanda rikicin Boko Haram ya 'dai'daita.

Rundunar ta ce tuni aka kafa wani kwamiti da ya kunshi jami'an bangarorin tsaro daban-daban na kasar, kuma ya yi nisa wajen tsara yadda za a mayar da aikin hannun 'yan sanda.

Hakan dai na faruwa ne yayin da sojoji ke ci gaba da kakkabe masu ta da kayar baya.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Solomon Arase ya shaida wa BBC sun soma bai wa 'yan sanda horo domin tunkarar wannan aiki