Dalibai na mu'amala da sa'o'in iyayensu a Biritaniya

Wata manhajar da aka fi amfani da ita a Burtaniya ta ce tana da dalibai mata kusan 250,000 da ke mu'amala da maza attajirai da suka kai tsaran iyayensu.

Manhajar ta ce ta samu karuwar dalibai 'yan matan da ke so a hada su da attajiran da kashi 40 cikin dari, a shekarar 2015.

An cimma alkaluman ne ta hanyar sakon email da suke bayarwa, saboda haka akwai yiwuwar mutum guda ya mallaki fiye da email daya, yayin da kalmar dalibai ta kunshi ma'aikata na wucin gadi da kuma wadanda suke samun horo.

Kamfanin manhajar yana hada 'yan mata ne da maza masu kudi da suka kai sa'oin iyayensu ko ma kakanninsu.

Kamfanin ya ce masu amfani da shi "za su samu damar yin rayuwa cikin daula tare da masu hannu da shuni akai-akai."

'Yan matan da suka shiga wannan harkar a baya-bayan nan sun hada da daliban da suka fito daga jami'ar Portsmouth da ta Kent a Ingila.

Masu manhajar sun yi amanna cewa tsadar kudin makaranta da na masauki ko dakunan kwana ne yasa daliban ke neman hanyoyin samun kudi a lokacin da suke karatu.

Sai dai abin da bai fito fili ba shi ne ainihin yawan masu amfani da manhajar nawa ne ke mu'amala da juna a zahiri.

Wasu alkaluman da aka fitar a watan jiya sun nuna cewa, an samu karuwar aikata manyan laifuka da ake dangantawa da irin wadannan manhaja na neman masoya.

Haka kuma manhajojin na janyo karuwar yada cututtukan da ake dauka ta hanyar saduwa.

Sashen turanci na BBC, Newsbeat ya yi hira da Clover Pittilla mai shekaru 20 a duniya, kuma 'yar asalin Bournemouth wadda ke amfani da manhajar.

"Ba jigari-jigarin mutane ne ne ke harkar ba, mutane ne da suke da abin duniya wadanda kawai holewa suke nema."

Da aka tambaye ta ko ya batun tarayya fa da wadannan mazaje sa'oin iyayensu, sai ta ce mutanen da ke amfani da manhajar na yin magana gar da gar idan batun ya taso.

Clover ta ce "A mafi yawancin lokuta su kan yi maka maganar ba boye-boye, idan abin da suke so kenan."

"Amma idan sha'awa ce kawai ko kuma dai wani abin ne daban, kuma ke kika nuna baki damu ba shike nan."

Abin da suke yin dai tamkar karuwanci ne duk da abin da Clover ta ce da kuma yawan daliban da ke amfani da manhajar.

Sai dai Clover ta musanta hakan "Wasu na tunanin hakan, amma ba haka ba ne domin idan baka so babu abin da zai faru."