Mun kama mai taimaka wa kungiyar IS a Kano — SSS

Jami'an tsaron Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jami'an tsaron Najeriya

Hukumar tsaron farin kaya ta Nigeria watau SSS ta ce ta kama wani dalibin jami'a wanda take zargi yana daukar matasa domin su shiga kungiyar IS da ke Iraki da Syria.

Hukumar SSS ta kama Abdussalam Enesi Yunusa ne a ranar 17 ga watan Janairu a birnin Kano, bayan da ya yi kokarin tafiya sansanin IS a Libya tare da wasu mutane da ya dauka.

Wata sanarwa daga hukumar SSS ta ce Yunusa na daga cikin gungun 'yan ta'adda da suke samun tallafin wani dan kasar Sudan wanda ke yi wa kungiyar IS aiki a yankin yammacin Afrika.

Sanarwar ta ce Yunusa dalibi ne a jami'ar kimiya da fasaha ta Minna a jihar Neja.

A cewar hukumar ta SSS, an kama wasu mutane wadanda su ma ke da alaka da kungiyar ta IS.

Tun a bara ne, kungiyar Boko Haram a Najeriya ta yi mubaya'a ga kungiyar IS sannan ta sauya sunanta ya koma kungiyar IS ta Yammacin Afrika.

Dama dai wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Kobler ya ce kungiyar IS ka iya kara karfi a Afrika ta yadda za ta hade da kungiyar Boko Haram a Nijar da Chadi da Najeriya.

A wani labarin kuma, hukumar ta SSS ta ce, ta kama mutane biyar wadanda ta ce suna shirin kai hare-haren ta'addanci a wasu jihohin arewacin Najeriya.