Hilary Clinton ta dauki mataimaki

Hilary ta zabi Kaine a matsyin mataimaki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hilary ta zabi Kaine a matsyin mataimaki

'Yar takarar shugabancin Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton, ta sanar da wanda zai tsaya a matsayin mataimakinta a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba.

Kamar dai yadda aka yi ta hasashe, ta zabi Sanata Tim Kaine, wanda wakiltar jihar Virginia a majalisar Dattawa.

Misis Clinton ta yaba masa kan yadda yake sadaukar da rayuwarsa wajen kwato wa al'umma hakkokinsu.

A na sa ran bangaren Senator Kaine ya ce ya yi matukar farin ciki da aka tsayar da shi a matsayin mataimakin 'yar takarar, kuma tuni ya kosa su fara yakin neman zabe gadan-gadan.

Misis Clinton ta yi fatan samun kuri'ar jama'ar da basu yanke hukunci kan wanda za su zaba ba, da kuma 'yan jam'iyyar Republican masu matsakaicin ra'ayi da ba sa goyon bayandan Donald Trump, saboda Mista Kaine.

Sanata Kaine dai ya na jin harshen Sifaniya sosai, kuma ana ga zabinsa da Hilary ta yi wata farar dabara ce, domin kuwa zai iya janyo musu kur'iun Sifaniyawa mazauna Amurka da ke da yawan gaske.

Hilary Clinton dai ta jam'iyyar Democrat da mataimakin ta Tim Kaine, za su fafata da Donald Trump da mataimakin sa Mike Pence daga jam'iyyar Republican a zaben da za a yi watan Nuwmbar bana.

'Yan takarar biyu na zazzafar hamayya da ta kai su ga sukar ra'ayin juna a yakin neman zabe da zai kara kankama yanzu haka.