Facebook zai rinka watsa intanet ta jirgin sama

Facebook drone

Asalin hoton, drone

A birnin Arizona na Amurka, a karon farko, karamin jirgi mara matuki ya tashi sama a wani bangare na burin Facebook na samar da intanet ga miliyoyin mutane a yankuna masu wuyar kaiwa.

Tsarin shi ne jirgin mai aiki da hasken rana, zai yi shawagi a sama na wasu watanni, yana samar da intanet ga mutane a doron duniya.

Amma wannan tsari gaba dayan sa, a wata ma'aikata a Kudu maso Yammacin Ingila a ka kirkire shi.

Shekaru biyu da suka wuce, kamfanin Facebook ya saye ma'aikatar da ta kware wajen kera jirgi mara matuki. Ma'aikatar yanzu, ta kera jirgin farko na wannan tsari wato "project Aquila".

Injiniya Andy Cox, wanda ya sayar da ma'aikatar ga Facebook, shi ne jagoran wannan tsari.

Ya ce: "Jirgin zai yi shawagi a nisan a kafa 60,000 daga kasa zuwa sararin samaniya, inda yanayi ke da sanyi sosai, kuma zai yi shawagi har na watanni uku, yana watsa intanet da ake bukata.

Facebook drone

Asalin hoton, Facebook

Kodayake yana da fuka-fuki mai fadi irin na Boeing 737, nauyinsa bai wuce kashi daya cikin uku na karamar mota ba.

Amma sai nan da wasu shekaru ne wannan jirgi zai yi shawagi na watanni uku a sararin samaniyar kasashen Afirka, yana samar musu intanet. A halin yanzu, wasu kamfanoni za su kokarta yin irin wannan aiki.

Shirin Project Loon na kamfanin Google, ya hada ne da yin amfani da manyan balan-balan, na ganin mutane a yankunan da ba a iya shiga, sun samu intanet.

Sai dai, irin wannan aiki, yana tattare da takaddama inda kasar India ta ki amincewa da shirin Facebook na bai wa 'yan kasar damar shiga intanet ta wayoyin salula kyauta, inda ta ke zargin, shirin, wani yunkuri ne na sa Facebook ya kara karfi.

Mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya kosa don ganin tashin jirgin na farko domin wata rana wannan jirgin zai iya sa kamfaninsa ya kara shahara a harkar intanet a duniya.