'Kannywod ba za ta ci gaba ba sai an daina fina-finai maras Al-Qibla'

Bayanan bidiyo,

Kannywood ta rasa alkibla

Shahararren jarumin fina-finan Kannywood Aminu Sheriff, wato Momoh ya ce masana'antarsu ba za ta ci gaba da sai an daina yin fina-finan "da ba su da al-kibla".

Ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da BBC a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

"Babban kalubalen da muke fuskanta ita ce a samu manufa daya ko wata taswira da za a shata domin kai masana'antar Kannywood ga ci gabanta da kuma bunkasar harshen Hausa.

"Idan za a ci gaba da yin fina-finan da ba su da al-kibla, babu inda za a kai", in ji jarumin.

Aminu Sheriff, wanda ya ce babbar manufarsa ta soma fim ita ce a watsa harshe da al'adun Bahaushe a kasashen duniya, ya kara da cewa: "idan ba za mu iya yin hakan ba, babu riba a harkar Kannywood."

Jarumin, wanda ke gabatar da wani shiri kan fina-finai a wani gidan talbijin, ya wanke kansa daga zargin da ake yi masa cewa ya tozarta wata 'yar fim a shirin nasa lokacin da ya yi mata tambayar da ake gani ba ta shafi harkar fim ba.

A cewarsa, ya yi wa Umma Shehu tambaya kan addinin Musulinci ne bayan ta bayyana masa cewa ba ta damu da kallon fina-finai ba saboda tana zuwa makaranta.

Momoh da Ali Nuhu sun fito a fina-finai da dama tare

Asalin hoton, Instagram/Aminu Sheriff

Bayanan hoto,

Momoh da Ali Nuhu sun fito a fina-finai da dama tare

"Abin da ya sa na yi mata tambaya kan addini shi ne, na ga ana yawan yabawa 'yan fim maganganu cewa ba sa zuwa makaranta, ba su da ilimi musamman na addini ballantana na boko.

"Da na ji ta ce ba ta damu da kallon fim ba saboda tana zuwa makaranta sai na samu karsashin nunawa masu yi mana irin wancan kallo cewa 'bari na tambaye ta kan addini domin ta nuna musu cewa ba duka aka taru aka zama daya ba'.

"Kuma ina ganin fahimta ce mutane ba su yi ba shi ya sa suke ganin kamar ba ta amsa tambayar da na yi mata ba", in ji jarumin.

Umma Shehu

Asalin hoton, Instagram/UMMA SHEHU

Bayanan hoto,

Hirar da suka yi da Umma Shehu ta janyo ce-ce-ku-ce

Aminu Sheriff, wanda ya soma fim sama da shekara 20 da suka wuce, ya fara ne da rubuta fina-finai kafin ya soma fitowa a matsayin jarumi.

Ya rubuta fina-finai irinsu Mugun Nufi, A yi dai Mu Gani da Dr Gulam.

Fim din da ya soma fitowa a ciki shi ne 'Al-Mustapha' wanda suka fito tare da fitaccen jarumi Alhaji Kabiru Maikaba.

Momoh

Asalin hoton, Instagram/Aminu Sheriff

Bayanan hoto,

Burina shi ne a bunkasa harshen Hausa - Momoh

Momoh ya kwashe sama da shekara 20 yana fim

Asalin hoton, InSTAGRAM/Aminu shariff

Bayanan hoto,

Momoh ya kwashe sama da shekara 20 yana fim