Burina na zama limami - Alfa Ibrahim

Burin Alfa Ibrahim, wanda malamin makarantar Allo ne a Abuja, shi ne ya zama babban limamin garinsu a jihar Naija, wanda hakan shi ne gadon gidansu.

Ya yi wa shirin BBC Hausa na ''Burina,'' bayani kan yadda yake son wannan buri na sa ya cika.

Ku ma za ku iya turo mana bidiyo ko muryar da kuka nada ta lambarmu ta WhatsApp 08092950707.