"Mutum daya ne ya kai hari Munich"

Mutum daya ne ya kai harin
Bayanan hoto, Mutum daya ne ya kai harin

'Yan sanda a kasar Jamus sun ce wani matashi Bajamushe dan asalin kasar Iran ne ya kai hari a birnin Munich, ya kashe mutane tara, yayin da 16 kuma suka jikkata.

Matashin mai shekaru 18, na daga cikin wadanda su ka mutu, kuma ana kyautata zaton shi ya kashe kansa.

Shugaban 'yan sandan birnin na Munich Hubertus Andrae ya ce ba bu wasu bayanai na barazana dangane da matashin, kuma ba a san dalilinsa na kai harin ba.

A yanzu dai tuni aka bude tashoshin jiragen kasa, bayan da aka rufe su na wasu sa'o'i sakamakon fargabar kara kai hare-hare.

An dai kai harin ne a rukunin shaguna na Olympia, a lokacin da jama'a ke tsaka da hada-hada.

Cikin wadanda harin ya rutsa da su har da kananan yara.

Jirage masu saukar ungulu sun dinga yin shawagi a birnin bayan harin, yayin da kuma aka futo da 'yan sandan ko-ta-kwana.

Jami'an tsaro sun dade a cikin shirin ko-ta-kwana tun lokacin da wani yaro ya raunata mutane biyar a wani jirgin kasa ta hanyar amfani da wuka.

Kungiyar IS da ke da'awar kafa daular Musulunci ta dauki alhakin harin na jirgin kasa.

Hukumomi sun yi gargadin cewa za a iya sake kai hare-hare a kasar.