Dalilai huɗu da suka sa BBC Hausa yin zarra —Pate

  • Haruna Shehu Mjos
  • BBC Hausa
Umaru Pate

Asalin hoton, Nta

Bayanan hoto, Farfesa Umaru Pate

Yayin da BBC Hausa ke ci gaba da bukukuwan cikarta shekara 60, wani masani a harkar yada labarai, Farfesa Umaru Pate ya ce abubuwa hudu ne suka sa kafar ta shiga gaban saura.

Da yake jawabi a wajen wani taro da BBC Hausa ta shirya a Abuja Najeriya, Farfesa Pate ya ce mutane da yawa basa gasgata bayanai, muddin ba BBC Hausa ce ta rawaito su ba.

Ya ce dalilai hudu da suka kafar kece tsara, su ne:

  • Fadin gaskiya komin dacin ta:

Farfesa Pate, wanda shi ne shugaban tsangayar nazarin aikin jarida a jami'ar Bayero dake Kano, ya ce BBC Hausa ta yi fice a wurin jama'a na zama kafar da bata fargabar fadin gaskiya game da kowanne irin lamari, koma wanene kuma abin ya shafa. Wannan ya ce ya sa mutane da yawa idan suna so a dauki ancen da suke yi da gaske, suke cewa a BBC suka ji.

Farfesa Pate ya ce BBC Hausa tana samun kwarin gwiwar fadin gaskiya ne saboda babu wanda ke cewa me yasa ta yi haka, wato babu masu yi mata katsalandan a cikin aikinta.

  • Kwarewa da kuma ingantattun kayan aiki:

Abu na biyu acewar Farfesa Pate, shi ne kwarewar da ma'aikatan BBC Hausa ke da ita, da kuma yin amfani da kayan aiki masu nagarta. Ya ce masu sauraro suna so a rika kawo musu labari cikin hikima sannan suna so su rika sauraron labarai tangaran kamar a gabansu a ke karantawa. Wannan, ya ce ya sa mutane na son BBC Hausa saboda gamsuwa da suke samu daga wurinta.

  • Kawo wa jama'a labaran da suka shafe su:

Farfesa Pate ya ce abu na uku da ya sa BBC Hausa ta yi zarra shi ne, tana kawo wa masu sauraronta labaran da suka shafi rayuwarsu. Ya ce duk da cewa kafa ce ta kasa da kasa, amma duk kankantar lamari indai ya shafi rayuwar masu sauraronta, bata kawar da kai daga shi. BBC Hausa ta na kawo wa jama'a labaran ta suka shafe su, ba labaran da basu da alaka da rayuwarsu ba.

  • Tafiya da zamani:

Abu na hudu da Farfesa Pate ya ce ya sa BBC ta kai yadda take yanzu, shi ne tafiya da zamani. Duk hanyoyin da BBC za ta bi domin ganin ta samu isa ga masu sauraronta, ta na bi. Zuwan intanet ya sa BBC Hausa kasancewa na farko farkon rungumar hanyoyin kai wa ga matasa wadanda suka fi duba labarai ta wayoyinsu na salula. A koda yashe kuma, BBC Hausa na kara azama don ganin ta bi duk hanyoyin da suka dace na aikawa da bayanai ga masu jin harshen Hausa.

Farfesa Fate ya ce ya taso ne ya ga mahaifisa na sauraron BBC Hausa, kuma shi ma ya ci gaba da sauraron tare karfafa gwiwar dalibansa a jami'o'i a kan su rika sauraron BBC Hausa don su san yadda ake gudanar da aikin jarida yadda ya kamata.

Ya kalubalanci hukumomi a Najeriya da su tashi tsaye don gyara kafafen yada labarai na cikin kasar, saboda an bar su a baya.

BBC Hausa shekara 60
Bayanan hoto, BBC Hausa

Manyan mutane ne daga sassan Najeriya dama wakilan wasu kasashen waje suka halarci kasaitaccen taron bikin a Abuja.

Cikin mahalarta taron, akwai gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, da kakakin majalisar wakilan Najeriya, Mista Yakubu Dogara.

Babban wanda ya gabatar da makala a wurin shi ne Farfesa Abdalla Uba Adamu na jami'ar Bayero da ke Kano.

Domin ganin yadda taron ya kasance, ku ziyarci shafinmu na BBC Hausa Facebook