Bangladesh: HRW ta shawarci Facebook

Sheikh Hasina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firayiministan Bangladesh Sheikh Hasina

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi kira ga kamfanin Facebook da kada ya taimaka wa gwamnatin Bangladesh a yunkurin da take na rufe bakin masu sukarta.

Wata minista a gwamnatin Bangladesh ta ce ta na so shafin Facebook ya hana mutane wallafa bayanai masu aibanta wasu addinai da haddasa yamutsi a cikin al'umma.

Ministar ta zargi shafin Facebook da taimakawa wajen yaduwar ayyukan tsageru masu daukan bindiga.

Sai dai kungiyar Human Rights Watch ta bukaci shafin Facebook da kada ya amince da kudurin gwamnatin Bangladesh, domin hakan zai tauye wa mutane hakkin tofa albarkacin bakinsu.

A 'yan shekarun da suka gabata, an kashe masu wallafa bayanai a intanet da dama, wadanda babu ruwansu da abubuwan da suka shafi addini a kasar.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce gwamnati, ba ta na nufin kare mutane ba ne, da wannan kuduri da ta yi, sai dai don gudun yin batanci ga addinai.