'Yan majalisar dokokin Nijar mata sun zama dumama kujera'

Masu korafin sun ce matan sun zama dumama kujera

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu korafin sun ce matan sun zama dumama kujera

Wasu 'yan Jamhuriyar Nijar sun koka kan abin da suka ce rashin katabus din mata 'yan majalisar dokokin kasar ke yi a zauren majalisar.

Wasu da suka zanta da BBC sun ce yawancin mata 'yan majalisar dokokin ba sa gabatar da bukatun al'uma idan aka zo muhawara, suna masu cewa hasalima ba sa cewa ko uffan.

Shugabar matasa masu kare hakkin dan adam Falmata Muktar ta ce, "A cikin mata sha uku da ke majalisar dokokin babu wacce ke cewa komai. Idan ba za su iya ba ya kamata su bar majalisar mu aike da wasu."

Sai da wata 'yar majalisa, Honourable Hauwa'u Abande ta ce mata sun yi abin gani sosai a majalisar.

Ta kara da cewa za su ci gaba da yin ayyuka domin ci gaban kasar.